Jami’ar Ilorin ta karrama matasa masu yiwa kasa hidima su 3

unilorin new
unilorin new

Sashin adana bayanai da Ayyukan Jarabawa na Jami’ar Ilorin, a ranar Talata ya karrama matasa masu yiwa kasa hidima su 3 dake rukunin ‘A’ zubi na ‘1’ na shekarar 2021.

Masu yiwa kasar hidima su 3 sun kammala aikin hidimar kasar su ne na tsawon Shekara guda a sashen.

Mataimakiyar Magatakardar Jami’ar mai kula da sashin, Khadija Garba, an karrama matasan ne bisa kwazo da suka yi tare da jajurcewa ba tare da nuna san kai ba, a lokacin da suke gudanar da ayyukansu na hidimar kasa a sashin musamman wajen shigar da makin Jarabawa.

Khadija Garba ta ce irin gogewa da matasan suka samu, tare da ilimin da suke da shi zai kai su ga matsayi mafi girma na nasara.

Ta ce mambobin ‘Yan hidimar kasar sun yi aiki mai kyau da ya gamsar da kowa a cikin shekara guda ta hidimar kasar su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here