Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa sabbin kwalejojin fasaha guda uku a Najeriya domin cika aniyarsa ta samun Ilimi cikin sauki .
Darakatan yada labarai na ma’aikatar Ilimi ta kasa, Mr Ben Bem Goong shi ne ya sanar da hakan cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai a Abuja.
Sanarwar tace sabbin kwalejojin guda uku za a samar dasu ne a Umunnoechi ta jihar Abia, da guda daya a yankin Orogun na jihar Delta sai Kuma guda daya a Kano.
Yace ana sa ran za a fara daukar darasi a sabbin kwalejojin cikin watan Oktoba na shekarar 2022.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa zuwa yanzu ana da kwalejojin fasaha guda 36 kenan a Najeriya.