Gwamna Yusuf ya sake jaddada kudurin goyon bayan shirin (Renewed Hope Agenda) don bunkasa harkar wasanni

IMG 20260509 WA0558 750x430

Gwamna Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na goyon bayan shirin Saabunta Fata (Renewed Hope Agenda) musamman ta hanyar habaka wasanni a matsayin wani mataki na hadin kai, zaman lafiya da cigaban kasa.

Gwamnan, wanda Mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo ya wakilta, ya bayyana hakan a cikin jawabin da ya gabatar a matsayin Bako na Musamman a bikin rufe gasar kwallon ƙafa ta Northwest Veterans All-Stars Renewed Hope Novelty da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a jihar Kano, a ranar Asabar.

An shirya taron ne domin girmama Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa, Alhaji Shehu Dikko.

Gwamna Yusuf ya yaba wa masu shirya taron, ƙungiyoyin da suka shiga gasar, magoya baya, da duk masu ruwa da tsaki da suka sa taron ya yi nasara sosai.

A cewarsa, kwallon kafa na zama dandali mai karfi na hada mutane ba tare da la’akari da kabila, addini, siyasa ko matsayi na zamantakewa ba, yana mai jaddada cewa ruhin aiki tare da mutunta juna da aka nuna a wasan yana nuna dabi’un da ake bukata domin karfafa al’umma.

Ya yabo wa sofaffin ‘yan wasa da sauran manyan mutane kan ci gaba da jajircewarsu wajen gina kasa, duka a lokacin da kuma bayan sun gama hidima, inda ya bayyana su a matsayin abin koyi ga matasa.

Ya kara bayanin cewa shirin Sabunta Fata na nufin gina kasa mai karfi da wadata ta hanyar karfafa shigar matasa, rayuwa mai lafiya, huldar jama’a da zaman lafiya tare.

“Abubuwa irin wannan suna karfafa shigar matasa, rayuwa mai kyau, hulda da jama’a, da zaman lafiya, wadanda su ne ginshikan da ake bukata domin cigaban kasa,” in ji Yusuf.

“Ga ‘yan wasan, kun fito ne a matsayin masu nasara a yau domin kun nuna jarumta, sha’awa, da kyakyawan dabi’ar, suma masu shirya taron, na gode muku da kirkirar dandali da ke samar da hadin kai da cigaban al’umma ta hanyar wasanni.

“Kamar yadda muke kammala wannan taron mai cike da tarihi, yana da kyau mu ci gaba da rike dabi’un zaman lafiya, hakuri, da hadin kai.” In ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here