Wata kungiya mai zaman kanta, (Dr. Dahiru Muhammad Hashim Foundation) a ranar Asabar ta tallafa wa mata da matasa 1,426 a Karamar Hukumar Dala ta Jihar Kano da kayan fara kasuwanci da tallafin kudi.
Da yake gabatar da kayayyakin a Kano, wanda ya kafa gidauniyar, Dr. Dahiru Muhamma Hashim, ya ce wannan tallafin da nufin taimakawa don su zama masu dogaro da kansu da inganta rayuwarsu.
SolaceBase ta ruwaito cewa Muhammad Hashim, wanda shi ne Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, ya ce wannan tallafin na daga cikin Shiri na Musamman na Tallafawa jama’a shekarar 2026 na gidauniyar da kaddamar da shirin sabunta fata ga matasa.
Rabon tallafin, wanda aka gudanar a Filin Shinge Kurna, an raba kekunan dinki, babura, injinan sarrafa taliya, injinan nika, da tallafin kudi ga masu amfana domin taimaka musu kafa kasuwanci mai dorewa.
Da yake jawabi a wajen bikin, Dr. Hashim ya ce wannan shiri ya yi daidai da tsarin ci gaba a matakin kananan hukumomi na gwamnatin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
A cewarsa, gwamnati ta himmatu wajen gina al’umma da samar musu hanyoyin dogaro da kai domin samun damar inganta rayuwarsu.
“Wannan shirin tallafawa zai ci gaba da yardar Allah, wadanda suka amfana su tabbata sun yi amfani da kayayyakin cikin hikima su kuma bunkasa kansu ta hanyar kasuwancin,” in ji shi.
Muhammad Hashim, wanda shi ne kuma Kwamishinan Albarkatun Ruwa na rikon kwarya, ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da shirin ga mazauna yankin Gobirawa da karamar hukumar Dala.
Kwamishinan ya kuma taya Ali Madaki da Lawan Usaini murnar zama ‘yan takara na Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Ya ce masu ruwa da tsaki a Dala sun dauki mataki daidai ta hanyar tallafa wa takarar ta su.
Daga cikin kayayyakin da aka raba akwai kekunan dinki 106, babura 20, injinan sarrafa taliya 100, da injinan nika 100, tare da sama da Naira miliyan 20 a matsayin tallafin kudi ga masu amfana.
A jawabinsa, Shugaban APC na Karamar Hukumar Dala, Alhaji Dayyabu Ahamed Mai Turare, ya yaba wa kwamishinan kan wannan shiri kuma ya bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin da aka ba su yadda ya kamata.
“Wasunku ba ku da kasuwanci a baya, amma da wannan tallafi da yawa daga cikinku yanzu kuna da hanyar samun kudin shiga. Ina rokonku kada ku sayar da kayayyakin ku yi amfani da su domin amfanin ku,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kano kan abin da ya kira mulki mai kyau a jihar.
Daya daga cikin wadanda suka amfana, Aisha Sale Bala, ta bayyana godiyarta ga kwamishinan kan tallafin, tana mai cewa wannan kyauta ta zo daidai lokaci kuma tana da tasiri.
Haka zalika, Marakisiya ita ma wata da ta amfana, ta gode wa kwamishinan kan wannan shiri.
Bikin ya ja hankalin masu ruwa da tsaki na siyasa, shugabannin al’umma, da manyan baki daga ko’ina cikin Karamar Hukumar Dala da sauran sassan jihar.











































