Dangote Ya Zo Jihar Lagos Shekaru 45 da Suka Wuce Ba Shi da Komai – Gwamna Sanwo-Olu 

Sanwo olu and Dangote 750x430 1
Sanwo olu and Dangote 750x430 1

Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya yabawa shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote bisa kirkirar matatar mai a Najeriya musamman jihar Lagos. Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin da yake Magana a bikin kaddamar da matatar a ranar Litinin 22 ga watan Mayu.

Yace Dangote ya zo jihar Lagos daga Kano shekaru 45 da suka wuce ba shi da komai, amma yanzu ya samar da abubuwan da za su sanya Nahiyar Afrika alfahari.

“Labari na farko shine na wani matashi dan Najeriya shekaru 45 da suka wuce, wanda ya zo jihar Lagos daga wani babban birni, Kano babu komai amma ya duba bambance-bambancen da muke da shi ya gina shahararren kamfani mai girma ga Afirka.”

Matatar Dangote wanda ta na karkashin babban kamfanin Dangote da ke samar da kayan masarufi daban-daban an kaddamar da ita yau a jihar Lagos. Kamfanin wadda ya ke Ibeju-Lekki zai samar da danyen mai zuwa Nahiyoyi da dama da suka hada da Afirka da Asia da kuma Amurka.

Sannan zai samar da litan mai miliyan 38 na man fetus da bakin mai da kalanzir da kuma man jiragen sama ga Najeriya a kullum, cewar jaridar.

Matatar har ila yau za ta samar da ganga 650,000 na danyen mai wanda za a sarrafa shi zuwa bakin mai da gas da kalanzir da kuma mai da jiragen sama suke amfani da shi.

Matatar da ke Ibeju-Lekki a jihar za ta fitar da litan man fetur miliyan 38 da kuma bakin mai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here