Gwamnatin Jihar Kwara a ranar Laraba ta sanar da cewa wadanda aka sace a lokacin harin da aka kai wa garuruwan Woro da Nuku a Karamar Hukumar Kaiama a ranar 3 ga Fabrairu, 2026, sun shaki iskar ‘yanci.
An sanar da wannan ci gaba ne a ranar Laraba a shafin Facebook na Gwamnatin Jihar Kwara, watanni bayan an sace mutane 176.
Gwamnatin ta rubuta cewa, “Alhamdulillah, muna godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR, jami’an tsaro da duk wanda ya taka rawa wajen cimma wannan babban nasara. Muna godiya!”
An sace wadanda abin ya shafa ne lokacin da wasu ‘yan ta’adda da ake zargin suna da alaka da Boko Haram suka mamaye kauyukan Woro da Nuku da babura, suka kai hari mai tsanani wanda ya dauki sa’o’i da dama.
Harin, wanda ake ganin shi ne daya daga cikin hare-haren da suka fi muni a tarihin Jihar Kwara, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200, ya raunata wasu da dama, ya lalata gidaje da kasuwanci, sannan ya tilasta wa mazauna yankin guduwa.
An ce ‘yan sintiri na cikin gida da suka yi yunkurin fuskantar maharan sun kasa, inda wasu daga cikinsu aka ce an kama su aka kone a cikin ofishinsu.
Har yanzu ba a samu karin bayani kan yadda aka sako wadanda aka sace din ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.












































