Super Eagles sun bude sansani a Warsaw, Poland, a shirye-shiryen da suke na wasannin sada zumunci na kasa da kasa da Poland da Portugal.
Bayan nasarar da suka samu a gasar Unity Cup ta 2026 a Landan, Super Eagles sun isa Poland da safiyar ranar Litinin.
Jami’in yada labaran tawagar, Promise Efoghe, ya tabbatar da cewa ’yan wasa 18 sun isa sansani yazuwa lokacin rubuta wannan rahoto.
Efoghe ya ce ’yan wasa 16 daga cikin 18 sun halarci atisaye na farko da tawagar a Poland a yammacin ranar Litinin.
Mai Horarwa Eric Chelle ya tabbatar da cewa ba a sa ran taurarin ’yan wasa Victor Osimhen da Ademola Lookman za su shiga cikin tawagar ba.
Chelle ya ce an baiwa Victor Osimhen lokaci don warware makomar sa a kulob dinsa, yayin da Atletico Madrid ta nemi a ba Ademola Lookman damar hutawa bayan kakar wasa mai cike da gajiya.
Super Eagles za su fafata da Poland a ranar Laraba, 3 ga Yuni a Warsaw, sannan su buga da Portugal a ranar Laraba, 10 ga Yuni, a Leiria, Portugal. (NAN)












































