An san Hajiya Hadiza da halinta na raha da sadaukarwa ga sana’arta, kuma an ce ta rasu da safiyar ranar Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya.
Labarin rasuwarta ya yadu cikin sauri a tsakanin ’Yan Jarida da kewaye a ranar Litinin, lamarin da ya bar ’yan jarida da ma’aikatan hada labarai da abokan huldarta cikin kaduwa.
Abokan wuldarta sun bayyana lamarin a matsayin mai radadi, inda suke cewa rashinta za a ji sosai a tsakanin ’yan jarida bayan kusan shekaru ashirin da take hidimar abinci ga ’yan jarida da al’umma baki daya.
Tsawon shekaru, wurin sayar da abincin Hajiya Hadiza ya kasance bs wurin cin abinci kawai ba. Ya zama wurin taro inda ’yan jarida, editoci da baki ke taruwa don cin abinci, tattaunawa da hutawa yayin da suke tsara aikace-aikace.
Sama da rawar da ta taka a matsayin mai sayar da abinci, an kuma san ta da samar da damar aiki ga matasa mata, da yawa daga cikinsu sun koyi abubuwa masu amfani da zai taimake su a rayuwa dobln dogaro da kan ta hanyar kasuwancinta.
Wasu ’yan jarida da suka yi tsokaci kan lamarin sun bayyana kyautatawarta, karamci da kuma halin uwa da take da shi. Sun kuma bayyana cewa tana girmama abokan cinikinta tana kuma da kyakkyawar alaka da mutane.
Mambobin Cibiyar ’Yan Jarida ta NUJ sun bayyana ta a matsayin a matsayin muhimmiyar bangare ta wurin, suna cewa gudunmawar da ta bayar tsawon shekaru ta taimaka wajen tsara yanayin zamantakewar ’yan jarida. Sun kuma roki Allah Madaukaki ya yafe mata kura-kuranta kuma yasa ta hutu a makwancinta
Yayin da ake ci gaba da ta’aziyya, mutane da dama na cewa aikin alherin Hajiya Hadiza zai ci gaba da rayuwa ta hanyar rayukan da ta taba, matan da ta karfafa, da kuma abubuwan tunawa da ta bari ga tsararrakin ’yan jarida.












































