Rahoto na Musamman: Me ya sa wakokin siyasa ya kamata su tallata ra’ayoyi, ba zagi ba

IMG 20260803 WA0127 750x430

Wakokin siyasa sun kasance wani bangare na dimokuradiyyar Najeriya tun bayan samuwar siyasar jam’iyyu. Sun taimaka wajen wayar da kan masu kada kuri’a, bayyana manufofin jam’iyyu, yabon jagoranci nagari, kuma a mafi kyawunsu, suna zama wata hanya da bin diddigin ayyuka.

Farfesa Soji Alabi na Jami’ar Legas a cikin wani bincikensa kan yadda ake amfani da waka a zabe a Najeriya, wakar yakin neman zabe a tarihi ta taimaka wajen isar da ra’ayoyin siyasa, karfafa shiga zabe da nuna burin masu kada kuri’a.

Haka kuma ya yi gargadin cewa wakokin da ke haddasa tashin hankali ko kai hari na kai tsaye kan mutuncin wani, ba su da wuri a cikin dimokuradiyya mai kyau. Wannan gargadi yana bukatar a sake lura da shi yanzu.

Abin da ya tayar da wannan muhawara a yanzu shi ne wakar da mawakin siyasar Hausa Dauda Kahutu Rarara ya fitar yayin shirye-shiryen zaben gwamnan Jihar Gombe na 2027.

An soki wakar sosai daga malaman addini, ‘yan siyasa, malamai da masu amfani da kafafen sada zumunta, inda hankali ya koma kan yadda ake gudanar da yakin neman zabe maimakon batutuwan siyasa.

Rikicin da ya dabaibaye wata waka ta kai hari da ake zargin ‘yan siyasa ne suka dauki nauyinta a Jihar Gombe ya nuna yadda sadarwar siyasa zata iya karkata daga manufarta ta gaskiya.

Maimakon gabatar da dalilan da yasa wani dan takara ya cancanci goyon bayan jama’a, ana cewa wakar ta zargi abokin hamayya da shan miyagun kwayoyi da cin hanci da rashawa yayin da take yabon wani dan takara.

Ko zargin gaskiya ne ko ba gaskiya ba, ba batu ba ne, yakin neman zabe ya kamata ya shawo kan masu kada kuri’a da gaskiya, tarihi da ra’ayoyi, ba zarge-zarge marasa tushe da aka lullube su cikin waka mai dadi ba.

Kai hari na kai tsaye da Rarara ke yi a wakokin siyasa ba yau ya fara ba. Masu sharhi sun gano cewa hakan ya fara ne a farkon shekarun 2010 lokacin da ya shahara ta hanyar wakokin kai hari ga Gwamnan Jihar Kano Ibrahim Shekarau lokacin yana tare da tsarin Kwankwasiyya.

A shekarun bayan nan, ya kuma juya harinsa ga tsoffin abokan siyasarsa, ciki har da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Ibrahim A. El-Caleel, mai sharhi kan al’amuran jama’a, ya rubuta cewa aikin Rarara ya nuna yadda wakar siyasar domin samun kudi ta koma daga tallafa ra’ayi da shirye-shirye zuwa zagin ‘yan hamayya, sau da yawa bisa ga muradun masu daukar nauyinta.

Farfesa Abdallah Uba Adamu na Jami’ar Bayero, Kano a cikin babban bincikensa kan wakokin siyasar Dauda Kahutu Rarara na da alaka da dogon tarihin daukar nauyinsa don cin mutunci.

Ya kawo misalai kamar Zuwan Maimalafa Kano, Malam Ya Yi Rawa Da Alkyabba da Tangal-Tangal a matsayin wakokin da aka gina su ne kan zagi, wulakanci da shagube na siyasa.

Ya Karkare da cewa, maimakon kasancewa waka ta adawa wadda ta dogara kan akida ko muradun jama’a, yawancin wadannan wakokin kawai suna nishadantarwa yayin da suke rage darajar wadanda ake kaiwa hari.

Wannan bambanci yana da muhimmanci. Najeriya na da tarihi mai girma na wakokin siyasa dana adawa.
Ayyukan Sa’adu Zungur, Akilu Aliyu, Abba Maikwaru da sauran fitattun mutane sun kalubalanci rashin adalci, mulkin mallaka da rashin kyawun mulki.

Wakokinsu sun tallafa ra’ayoyi kuma sun zaburar da wayar da kai kan siyasa, shi yasa ake ci gaba da tuna da su saboda sun yi magana kan burin al’umma, ba don su zagi mutane ba.

Tarihi ya kuma nuna cewa ba dole wakar yakin neman zabe ta koma zagi ba domin ta yi tasiri kan ra’ayin jama’a.

Alabi ya kawo misalin motsin ‘O To Ge’ (ma’ana ya isa) na Jihar Kwara a 2019 wanda ya hari daular Saraki a matsayin misalin yadda waka ta bayyana takaicin jama’a kan rinjayen siyasa tare da wayar da kan jama’a kan sauyi a dimokuradiyya.

Ko mutum ya yarda ko ba ka yarda ba, babban sakonta ya shafi mulki da sabunta tsarin shugabanci ba wulakanta mutum ba.

Ba za a iya cewa alakantawakai tsaye ba, wakokin da manufarsu ta farko ita ce wulakanta mutum, kirkiro sunayen banza ko maimaita zarge-zarge domin haddasa kyama a tsakanin jama’a.

Wadannan wakokin na iya yaduwa a kafafen sada zumunta, amma suna rage darajar muhawarar dimokuradiyya. Suna koya wa magoya baya su ki abokan adawa maimakon su duba ra’ayoyi daban-daban kan ilimi, kiwon lafiya, tsaro, aikin yi da ci gaban tattalin arziki.

Alhakin ba wai na mawaka ba ne kadai, ‘yan siyasar da ke daukar nauyin wadannan ayyuka su ma suna da alhaki.

Mawaki yana yin abin da mai daukar nauyi yake so ya biya masa. Idan yakin neman zabe ya fi maida hankali kan wulakanta mutum fiye da isar da manufofi, yana aike sako mai hatsari kan irin jagorancin da suke son bayarwa.

Akwai wani darasi da ‘yan siyasa bai kamata su manta da shi ba. Yakin neman zabe ta hanyar zagi ba koyaushe yake kawo sakamako mara kyau ga wanda aka yi niyya ba.

Yushau A. Shuaib, kwararre kan harkokin jama’a, ya ce harin da aka kai wa Farfesa Isa Ali Pantami kwanan nan ya haifar da tausayi a tsakanin ‘yan siyasa da na addini, har ya samu goyon bayan mutanen da ma ba za su bayyana ba.

Ko ka yarda da wannan magana gaba daya ko aa, ya nuna hadarin barin zagi ya maye gurbin shawo kan mutane da hujja. Masu kada kuri’a sukan gane yawan tashin hankali da zagi idan sun gani.

Wakar siyasa ta cancanci a ba ta daraja fiye da zama kayan aikin da ake haya domin zagi. Mawaka suna da tasiri mai girma kuma ya kamata su yi amfani da shi wajen tambayar masu mulki, tabbatar da cewa suna gudanar da aikinsu, yaba nasarori idan sun samu da kuma kalubalantar shugabanni su yi wa jama’a aikin da ya dace.

Yayin da yakin neman zabe ke kara kaimi zuwa ga zabe mai zuwa, jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da mawaka ya kamata su tuna cewa zabe gasa ce ta ra’ayoyi, ba gasar zagi ba.

Wakokin da ke wayar da kan ‘yan kasa suna karfafa dimokuradiyya. Wakokin da ke wulakanta ‘yan uwan kawai suna lalata ta ne.

Najeriya kuma tana bukatar dokar gudanarwa da zata ba da fifiko ga sadarwar siyasa da ta dogara kan batutuwa.

Kafafen yada labarai, kungiyoyin farar hula da Hukumar da ke Wayar da Kan Jama’a na Kasa su ma su tallafawa kamfen din da ke ba da lada ga kirkire-kirkire, gaskiya da ladabi, yayin da suke bayyana sakonnin da ke haddasa kyama ko dogaro da karya. Dimokuradiyya ta fi samun ci gaba idan an ci zabe ta hanyar shawo kan mutane da hujja fiye da wulakanta wasu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here