Majalisar dattawa ta kafa kwamitin mutum 7 wanda zai yi duba kan dokar cin zarafin jinsi

B98EE020 040D 4622 9F40 E08EECE858FF
B98EE020 040D 4622 9F40 E08EECE858FF

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya kafa kwamitin mutane bakwai kan dokar hana cin zarafin dalibai a manyan makarantu.

Majalisar ta zartar da kudirin ne a ranar 7 ga Yuli, 2020.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, mai wakiltar yankin Delta ta tsakiya ne ya dauki nauyin kudurin dokar.

An nada Sanata Micheal Opeyemi Bamidele (Ekiti ta tsakiya), a matsayin shugaban kwamitin taron.

Sauran mambobin sun hada da: Sanata Betty Apiafi, Stella Oduah, Abubakar Kyari, Suleiman Umar, Suleiman Abdu Kwari, da Kola Balogun.

Ana sa ran mambobin kwamitin taron za su gana da takwarorinsu na majalisar wakilai domin daidaita sassa biyu na kudirin da majalisun biyu suka amince da su a baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here