Hukumar kula da kayayyakin more rayuwa ta kimiyya da ƙere-ƙere ta kasa (NASENI) ta ce aikin ƙera jirgin sama mai saukar ungulu samfurin Najeriya na farko ya kusa kammalawa.
Hukumar ta yi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba jirgin zai fara jigila a sararin samaniya.
Manajan gudanarwa na Cibiyar bunkasa zirga-zirgar jiragen sama NASENI da ke Kaduna, Kareem Aduagba, ne ya bayyana hakan a jiya yayin wani taron tattaunawa da hukumar ta shirya, wanda ya samu halartar masu kirkire-kirkire da masana’antu daga cibiyoyin ilimi da masu zaman kansu a Kaduna, an yi shi ne domin inganta masana’antu na cikin gida, da kirkire-kirkire, da kuma karfafa kayayyakin da ake yi a Najeriya.
Taron ya tattaro jami’an gwamnati, da shugabannin masana’antu, da masu kirkire-kirkire domin tattauna manufofin da za su kawo ci gaban masana’antu da kere-kere a Najeriya.
Karin karatu: Bankin Kasar China Ya Ba Da Lamuni Dala Miliyan 254.76 Domin Titin Jirgin Kasa Daga Kano Zuwa Kaduna
Shugaban ya ce NASENI na kokarin bunkasa fasahar kere-kere ta gida don rage dogaron da kasar nan ke yi kan kayayyakin kasashen waje tare da samar da sabbin hanyoyin warware matsalolin da aka riga aka shimfida a sassa daban-daban.
Jagoran shirin, Saleh Kwaru, ya bukaci ‘yan Najeriya da su tallafa wa masana’antu na cikin gida, yana mai jaddada cewa ci gaban kasa ya dogara ne kan samar da kayayyakin amfaninta a gida.
Mukaddashin kodinetan shiyyar na hukumar kula da kananan sana’o’i ta shiyyar Arewa maso yamma (SMEDAN), Yusuf Suleman, ya yabawa hukumar bisa shirya taron domin magance kalubalen da ke kawo cikas ga kayayyakin da ake kerawa a cikin gida ta fuskar inganci da kamala.