Bankin raya kasar Sin ya sanar da amincewa da rancen $254.76m (€245m) don tallafawa aikin layin dogo na Kano zuwa Kaduna a Najeriya.
Wata sanarwa da aka fitar a shafin intanet na bankin a ranar Talata ta ce ana sa ran tallafin kudi zai tabbatar da ci gaba da aikin gine-ginen.
Ya bayyana a shafinsa na yanar gizo cewa, “Bankin Raya kasar Sin ya fitar a ranar Talata cewa, a kwanan baya bankin ya ba da rancen kudi Yuro miliyan 245 ($254.76m) ga aikin layin dogo na Kano zuwa Kaduna a Najeriya, tare da bayar da tallafin kudi domin ci gaban aikin.”