Masu son ficewa daga PDP za su iya yin hakan a yanzu – Saraki

images 3 1

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ce wadanda ke da niyyar ficewa daga jam’iyyar PDP a yanzu su fice domin baiwa masu goyon baya damar sake gina jam’iyyar adawa.

Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Kwara yana mayar da martani ne kan ficewa daga jam’iyyar PDP da ake yi, a wata sanarwa da da kansa ya sanyawa hannu a daren ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), tare da Ifeanyi Okowa.

Oborevwori ya gaji Okowa a matsayin gwamnan Delta bayan ya lashe zaben 2023 a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Saraki ya ce ya samu kiraye-kiraye da dama daga ‘yan jam’iyyar da abin ya shafa da kuma matasa masu goyon bayan dimokuradiyya kan sauya sheka da jam’iyyar PDP reshen jihar Delta ta yi a kwanakin baya.

Saraki ya bayyana cewa adawa mai karfi na da matukar muhimmanci ga dorewar dimokradiyya, inda ya kara da cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba a matsayin kasa mai jam’iyya daya ba.

Ya yi gargadin cewa tsarin jam’iyya daya, kamar yadda ake zargin wasu ‘yan siyasa ne suka shirya shi, yana da hadari ga kasa mai bambancin ra’ayi kamar Najeriya.

Tsohon gwamnan na Kwara ya bayyana halin da jam’iyyar PDP ke ciki a matsayin wadda za a sake ƙyanƙyasa, ya kuma yi kira ga ’yan uwa masu kishin kasa da su maida hankali.

Ya ce gara jam’iyyar ta samu ‘yan kishin gaskiya da jajircewa fiye da samun mabiya masu yawa kuma masu fuska biyu.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ya ce ya lura da rashin gaskiya a tsakanin wasu jiga-jigan ‘yan adawa kuma galibi ba zai iya amincewa da na kusa da su ba.

Saraki ya ce har yanzu PDP na da shekara biyu kafin zabe mai zuwa da za ta sake hadewa da kuma tsara dabaru.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba shugabannin jam’iyyar za su gana domin daukar wani muhimmin matsayi a kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here