Kungiyar PBAT Door-to-Door 2027 ta soki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, kan caccakar Shugaba Bola Tinubu game da hutunsa da yake yi a kasashen waje a halin yanzu.
Kungiyar ta bayyana kalaman Atiku a matsayin wani yunkuri na mayar da hutun shugaban kasa na yau da kullum ya koma takaddamar siyasa, tana mai jaddada cewa rashin shugaban kasar na dan lokacin ba yana nufin akwai gibi ko gaza jagoranci.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in gudanarwa na kungiyar na kasa, Sunday Asuku, ya fitar kuma aka raba wa manema labarai a jihar Kaduna ranar Lahadi.
Kungiyar ta bukaci Atiku da ya mayar da hankali wajen gabatar da tsare-tsarensa na siyasa ga ‘yan Najeriya gabanin babban zaben shekarar 2027.
Haka zalika, tafiyar ta bayyana Atiku a matsayin “gogaggen mai neman tsayawa takarar shugaban kasa mara tabbas,” tana mai cewa ‘yan Najeriya sun cancanci sanin ingantacciyar taswirar hanyarsa ta magance matsalolin kasar bayan yunkuri da dama da ya yi na ganin ya hau madafun ikon shugabancin kasar tun daga shekarar 1993.
Kaza-lika, ta zargi tsohon mataimakin shugaban kasar da rashin tsayawa a kan magana guda game da batun tallafin man fetur, inda ta tunatar da cewa ya yi yakin neman zabe a 2023 da alkawarin cire tallafin, amma yanzu yana fafutukar ganin an dawo da shi.
A cewar kungiyar, irin wannan matsayi za a iya kallonsa a matsayin yunkurin yin amfani da mawuyacin halin da ‘yan Najeriya ke ciki don samun moriyar siyasa.
“Bayan ya fito takarar shugaban kasa ba adadi tun shekarar 1993, ya kamata Atiku ya rika fada wa ‘yan Najeriya abin da ya yi niyyar yi daban, maimakon ya bata lokacinsa wajen sukar Shugaba Tinubu,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta ce ya kamata Atiku ya bayyana ko matsayinsa na yanzu kan tallafin man fetur yana wakiltar kyakkyawan tsari ne na manufofinsa ko kuma yunkuri ne na samun goyon bayan siyasa ta hanyar yaudarar ‘yan Najeriya da matsin tattalin arziki ya shafa.
Ta tuna wa Atiku cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta riga ta fara shirye-shiryen zaben 2027, tana mai karfafawa gwiwarsa da ya yi yakin neman zabensa ga ‘yan Najeriya kuma ya bayyana musu tsare-tsarensa na tattalin arziki, tsaro da samar da ayyukan yi.
“INEC ta fitar da jadawalin zabe. Ya kamata Atiku ya fita ya yi yakin neman zabe sannan ya fada wa ‘yan Najeriya abin da yake da shi domin su. Bata sunan Shugaba Tinubu saboda ya tafi hutu ba zai yi aiki ba,” in ji ta.
Kungiyar ta nanata cewa shugabannin kasa da sauran shugabannin duniya na tafiya hutu a kai-a kai kuma hakan baya nufin an yi watsi da harkokin gudanar da gwamnati ba.
Ta kara da cewa Najeriya tana da hukumomi masu aiki da jami’an da ke da alhakin tabbatar da dorewar gudanar da mulki a duk lokacin da shugaban kasar “ba ya nan.”
Kungiyar ta bukaci ‘yan Najeriya da su auna Tinubu bisa la’akari da manufofinsa da ayyukansa maimakon kalaman siyasa na baki kawai.
Haka kuma ta kalubalanci ‘yan siyasar adawa da su gabatar da ingantattun hanyoyin da za su taimaka wa gwamnati maimakon mayar da hankali kan abin da ta bayyana a matsayin yunkurin cin gajiyar kalubalen kasar domin samun nasara a zabe.












































