Yanzu-yanzu: Gwamnan Jihar Filato Mutfwang ya ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 24

Gwaman, Jihar, Plateau, dokar, hana fita,
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a iya karamar hukumar Mangu da ke jihar nan take. Hakan na kunshe ne a cikin wata...

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a iya karamar hukumar Mangu da ke jihar nan take.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamnan, Gyang Bere ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan tabarbarewar tsaro a yankin.

Karanta wannan: AA Rano ya kaddamar da sabon dakin karbar magani a AKTH wanda Sanata Ibrahim Shekarau ya gida

Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamna Mutfwang ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro da abin ya shafa.

“Ya bayyana cewa mutanen da ke kan muhimman ayyuka ne kawai ake barin su shiga cikin karamar hukumar har sai an samu sanarwa.

“Ya bukaci daukacin ‘yan kasa, musamman mazauna karamar hukumar Mangu da su bi wannan umarni tare da taimakawa jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihin bayanai domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Karanta wannan: Naira ta karu a kasuwar canjin kudade

“Ya koka da yadda har yanzu wasu mutane kan kuduri aniyar haifar da yanayi na rashin tsaro a jihar, duk da kokarin da gwamnati ke yi na kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda.

“Ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa da wadanda suka jikkata ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

“Ya yi alkawarin cewa za’a sake duba dokar hana fita da zarar an inganta tsaro yanda ya kamata.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here