Yanzu-Yanzu: NASU, SSANU za su tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani ranar Juma’a

SSANU NASU

Kwamitin hadin gwiwa na kungiyar Ma’aikatan da ba Malamai ba na Cibiyoyin Ilimi da Masu Hadinn Gwiwa (NASU) da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) sun tabbatar da fara yajin aiki a fadin ƙasa daga ranar Juma’a.

Kungiyoyin sun bayyana matsayarsu a cikin wata wasika mai kwanan wata 30 ga Afrilu, 2026, da aka aike wa Ministan Ilimi, Tunji Alausa, inda suka bayyana gazawar gwamnatin tarayya wajen kammala tattaunawar da ake ci gaba da yi da kuma gabatar da sabon tayi kan alawus-alawus.

Wasikar, wadda babban sakataren NASU, Peters Adeyemi, da shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim suka sanya wa hannu, ta ce yajin aikin zai fara daga karfe 12 na dare ranar 1 ga Mayu, 2026.

“Muna rubuto wannan don amincewa da karbar wasikarku kuma muna godiya ga mai girma Ministan Ilimi bisa janye wasikar da ta haifar da cece-kuce,” shugabannin kungiyar suka ce, suna magana kan takardar da ta gabata kan karin kashi 30 cikin dari na Alawus din kayan aikin da ba na Koyarwa ba (Consolidated Non-Teaching Tools Allowance). Inji shugabannin.

“Duk da haka, janyewar bai magance ainihin batutuwan da ke cikin takaddama ba.

Kungiyoyin sun kuma kara da cewa sakamakon tuntubar da aka yi shi ne cewa ba a biya bukatarmu ba dangane da jinkirin da ake samu a tsarin sake tattaunawar.

Kungiyoyin sun kara da cewa ba a gabatar da wani sabon tayi ba da zai maye gurbin alawus din da aka janye.

“Yayin da aka amince da wasikar janye Alawus din Kayan Aikin da ba na Koyarwa ba, ba a gabatar da wani sabon tayi ba da zai maye gurbin alawus na kashi 30 cikin dari da ke cikin wasikar da aka janye,” in ji su.

A cewar JAC, mambobi sun amince wa shugabannin daukar mataki idan gwamnati ta kasa kammala tattaunawar zuwa 30 ga Afrilu.

“Dangane da haka, tare da rashin kammala yarjejeniyar har zuwa 30 ga Afrilu 2026, kuma ba tare da wani sabon tayi ba, yajin aikin zai fara da ƙarfe 12 na dare ranar 1 ga Mayu, 2026,” wasikar ta karanta.

Kungiyoyin sun ce yajin aikin ya zama wajibi bayan abin da suka bayyana a matsayin rashin iyawar gwamnati na dakile rikicin ta hanyar tattaunawa mai ma’ana.

“Muna sanar da gwamnatin tarayya cewa sakamakon gazawarta na dakile yajin aikin ta hanyar amincewa da bukatunmu, dukkan mambobi za su fara cikakken yajin aiki ranar Juma’a, 1 ga Mayu, 2026,” in ji Adeyemi da Ibrahim.

Ana sa ran yajin aikin zai dakatar da ayyukan gudanarwa da na tallafi a manyan makarantun tarayya, wanda ke haifar da damuwa game da wani zagaye na kawo cikas a tsarin jami’o’in Najeriya, wanda ya fuskanci rikice-rikicen masana’antu akai-akai a ‘yan shekarun nan.

 

Cikakken bayani nan gaba…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here