JAMB ta bankado badakalar daukar dalibai miliyan daya ba bisa ka’ida ba

Jamb
Jamb

 

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta ce ta gano an shigar da dalibai da yawansu ya kai miliyan daya cikin wasu jami’o’i kasar nan ba bisa ka’ida ba.

A cewar hukumar, hakan na da nasaba da gazawar da wasu ‘yan takara suka yi wajen samun takardar shaidar shiga jami’o’in domin samun damar yi wa kasa wato NYSC na shekara 1.

Shugaban yada labarai na JAMB, Fabian Benjamin, a cikin wata sanarwa, a ranar Juma’a, ya ce an samu wannan adadi ne tun daga shekarar 2017 zuwa 2020.

Ya ci gaba da cewa: “Wannan jerin korafe-korafe ya samo asali ne daga takaicin da wadannan daliban suka nuna, kan yadda hukumomin da abin ya shafa ba su amince da karatunsu a hukumance.

“Saboda haka, Ministan Ilimi, Mall. Adamu Adamu, cikin tausayawa, ya amince da kashi na karshe na wadannan jarabawar da hannu.

Hukumar JAMB ta bukaci cibiyoyi da su gaggauta shigar da lambobin jarabawar, sunaye, darussan da suka dace, shekarar kammala karatunsu da sauran bayanan da suka wajaba na ‘yan takarar hukumar domin aiwatar da takardun neman amincewar ‘yan takarar.

 

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here