Sauyin Jam’iyyar Umahi: INEC za ta yanke hukunci kan umarnin kotu 

David Umahi 1 1 2
David Umahi 1 1 2

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta yanke hukunci kan umarnin kotu da kuma kudirori game da sauya shekar Gwamna Dave Umahi na Ebonyi da mataimakinsa, Cif Kelechi Igwe a mako mai zuwa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Okoye ya ce a cikin watanni uku da suka gabata, INEC ta shiga cikin sabbin kararraki 71 a kotuna daban-daban a fadin kasar, ciki har da shari’o’in da suka shafi sauya sheka da aka yi a jihar Ebonyi.

Ya kuma bayyana cewa an baiwa INEC umarnin kotu guda 10 da kuma gabatar da bukatar sauya sheka daga Umahi, Kelechi da ‘yan majalisar dokokin jihar su 16.

Okoye ya ce INEC ta yi taro ne a ranar Alhamis, inda aka tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da tashe-tashen hankulan da ba su shafi hukumar kai tsaye ba, amma inda manyan jam’iyyu suka shiga cikinta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here