Mutum 12 sun rasa ransu a hadarin mota a hanyar Neja

320934543 875002770594553 80440276375519394 n
320934543 875002770594553 80440276375519394 n

Rahotanni sun ce a kalla mutane 12 sun rasa ransu bayan da wasu manyan motoci biyu makare da waken suya da kantu suka yi taho mu gama a hanyar Lambata zuwa Agaie zuwa Bida.

Shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura a jihar Neja, Kumar Tsukwam, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce hadarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe biyar na safe.

Ya ce bayan afkuwar hadarin ta ke mutum 12 suka rasa ransu, yayin da wasu 10 kuma suka samu raunuka kuma tuni aka kai su zuwa asibitin Agaie don duba lafiyarsu.

Tsukwam, ya ce manyan motocin da suka yi hadarin na dauke da mutane 75 wadanda suka nufi jihar Legas daga arewa.

Ya kuma danganta afkuwar irin wadannan hadurra da gudun wuce kima da kuma rashin kiyaye dokokin hanya.

Daga nan ya ba wa masu ababan hawa shawara a kan su rinka takaita gudu da kuma kula da kiyaye ka’aidojin tuki da hanya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here