Jihar Neja ta saka dokar takaita zirga-zirga a wasu yankuna sakamakon rikicin kabilanci

Bago 750x430

Gwamnatin Jihar Neja ta saka dokar hana fita a wasu garuruwa da ke Karamar Hukumar Rafi biyo bayan sabon rikicin kabilanci da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi.

Gwamna Umaru Bago na Jihar Neja ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci garuruwan da rikicin ya shafa tsakanin kabilun Kamuku da Fulani a garin Tashar Bako, inda ya umarci jami’an tsaro da su tura dukkan kayayyakakin tsaron da ake da su zuwa yankunan a matsayin wani bangare na kokarin dawo da zaman lafiya da kuma dakile ci gaba da karya doka da oda.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana ce, wannan rikici na kabilanci ya samo asali ne daga takaddamar filin noma, kuma ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar rayukan mutane kusan 80.

Gwamna Bago, wanda mataimakinsa Mista Yakubu Garba ya wakilta, ya umarci hukumomin tsaro da su hanzarta rarraba dukkan kayan aikin da ake da su a fadin yankunan da abin ya shafa, inda ya kuma umarce su da su yi amfani da hanyoyin masu karfi da kuma na sulhu domin dakile rikicin da kuma hana shi bazuwa.

Gwamnan, wanda ya duba garuruwan da abin ya shafa tare da gano wuraren da suka fi fuskantar barazana, ya ce binciken farko ya nuna cewa takaddamar filin noma ce ta haddasa rikicin.

Ya umarci Sarkin Kagara, Alhaji Ahmad Garba Gunna, da ya kafa Kwamitin Zaman Lafiya da Sulhu domin saukaka tattaunawa, samar amana da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al’ummomin da abin ya shafa.

Haka kuma, Bago ya yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da masu fada a ji da su guji yada labaran karya ko wadanda ba a tantance ba, wadanda ka iya dagula lamuran tsaro. Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakan hana sake aukuwar hakan, sannan ya bukaci al’ummomin biyu da ke fada da juna da su rungumi zaman lafiya.
A cewarsa, al’ummomin biyu sun dade suna zaune tare cikin lumana tsawon shekaru, don haka kada su bari ayyukan wasu tsirarin mutane ya lalata dadaddiyar dangantakar da ke tsakaninsu.

Sarkin Kagara, Garba-Gunna, ya yaba wa gwamnatin jihar da hukumomin tsaro kan yadda suka dauki mataki cikin sauri domin shawo kan rikicin. Ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da baiwa jami’an tsaro hadin kai don dawo da zaman lafiya, yayin da ya gargadi ‘yan siyasa da kada su siyasantar da lamarin.
Ya jaddada cewa kada a fassara rikicin a matsayin fadan kabilanci tsakanin Kamuku da Fulani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here