An yi wa ma’aikatan shari’a biyu ritayar tilas, an rage wa alkalin Shari’a matsayi a Kano

Kano CJ Dije Aboki 750x430

Hukumar kula da ma’aikatan shari’a ta jihar Kano (JSC) ta yi wa ma’aikata biyu na sashin shari’a ta jihar ritaya tilas, ta dakatar da wani magatakardan kotu ba tare da albashi ba, ta rage wa alkalin Kotun Shari’a matsayi, ta janye dakatarwar da aka yi wa wani alkali, sannan ta bayar da umarnin bincikar wani insifeton ‘yan sanda da ma’aikatan kotu biyu kan wasu batutuwa na daban da suka shafi ladabtarwa.

Wannan mataki na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya sanya wa hannu, bayan taron hukumar karo na 90 da aka gudanar a ranar 3 ga watan Yuli karkashin jagorancin Babban Alkalin Jihar Kano.

Ya ce hukumar ta duba rahotanni da shawarwarin Kwamitin Korafe-Korafe na Ma’aikatar Shari’a (JPCC) kan takaddun korafe-korafe da ladabtarwa da suka shafi alkalan Kotun Shari’a da ma’aikatan hukumar shari’a.

A cewar sanarwar, hukumar ta amince da wadannan matakai na ladabtarwa daidai da ikonta na tsarin mulki domin daukaka mutunci, rikon amana da kuma dawo da yardarm jama’a ga bangaren shari’a.

Hukumar ta umarci Alkali Aliyu Yahaya Muhammad, shugaban kotun shari’a ta Babeji, da ya yi ritayar tilas ba tare da bata lokaci ba bayan da Kwamitin Karbar Korafe-Korafe na Ma’aikatar Shari’a ya tabbatar da zargin cin hanci da rashawa a kansa dangane da karar mai lamba CV/474/2024 tsakanin Talatu Ibrahim da Muntari Abubakar Baguda.

Haka kuma ta umarci alkalin da ya mayar da kudi Naira 250,000, wadanda ta ce ya karba a matsayin cin hanci.

A wani lamari mai kama da wannan, hukumar ta dakatar da Ibrahim Ahmad Ibrahim, magatakarda a Kotun Shari’a ta Babeji, na tsawon watanni hudu ba tare da albashi ba bayan ya amsa cewa ya karbi wani bangare na kudin da ake zargin an karba a matsayin cin hanci.

Sanarwar ta kara bayyana cewa hukumar ta amince da ritayar tilas ga Muzambilu Ado, Mukaddashin Daraktan Yada Labarai da Kididdiga na Kotun Daukaka Kara ta Shari’a, biyo bayan binciken Kwamitin wanda ya gano kura-kurai masu yawa a takardunsa na karatu.

Bisa binciken hukumar, abubuwan da aka gano sun hada da canza bayanan karatu da kuma shiga Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya (Law School) ba tare da amincewar hukumar ba.

Hukumar ta kuma rage wa Alkali Usman Haruna Usman, Shugaban Kotun Koli ta Shari’a (Upper Sharia Court) da ke Goron Dutse, matsayi da daraja daya saboda sakaci bayan ya amince da a tura kudaden sayar da kadarorin gado a asusun banki na kashin kai na wani ma’aikacin kotu.

“Wannan matakin ya fitar da kudaden masu karar ga barazanar yin awon gaba da su,” in ji sanarwar, inda ta kara da cewa hukumar ta kuma tabbatar da janye dakatarwar da aka yi masa a baya daga ayyukan shari’a na tsawon shekara guda, yayin da ta yi masa gargadi mai zafi.

A wani lamarin na ladabtarwa daban, hukumar ta yi wa Alkali Abdullahi Wayya, Alkalin Babbar Kotun Shari’a ta Kasuwa, kashedi mai zafi game da yadda ya gudanar da beli a kara mai lamba CR/172/2022 tsakanin Kwamishinan Yan Sanda da Muhammad Musa Kadawa.

Sanarwar ta ce an sami alkalin da sakaci wajen kula da tsarin belin, wanda hakan ya yi sanadiyyar sakin wanda ake tuhuma ba tare da tantance sahihancin takardun mallakar fili/gida da aka mika a matsayin jinginar beli ba.

Hukumar ta kuma ba da umarnin cewa a kai rahoton Insifito Shehu Adamu ga Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Kano domin gudanar da bincike da yuwuwar daukar matakin ladabtarwa bayan bincike ya nuna cewa ya yaudari kotun ta hanyar tabbatar mata cewa an cika dukkan sharuddan beli kafin aka saki wanda ake tuhumar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here