Ringim ya bukaci Najeriya ta yi amfani da makamashin hasken rana don habaka masana’antu da samar da kayayyaki na cikin gida

IMG 20260725 WA0386 750x430

Wani masani a fannin fasahar sadarwa (ICT) kuma Babban Daraktan cibiyar fasaha ta ENGAUSA Global Tech Hub, Injiniya Mustapha Habu Ringim, ya yi kira ga Najeriya da ta amshi wani dogon tsari wanda zai sanya makamashin hasken rana ya zama hanyar habakar masana’antu, samar da kayayyaki a cikin gida, fito da sabbin kirkire-kirkire da canja fasalin tattalin arziki, maimakon kallonsa kawai a matsayin hanyar magance matsalolin wutar lantarki na kasar.

SolaceBase ta ruwaito, Ringim ya yi wannan kiran ne a yayin da yake jawabi a matsayin babban bako mai jawabi a wurin taron tattaunawa kan makamashin hasken rana na Kano (Kano Solar Dialogue), wanda aka shirya ta hannun Cibiyar Sabunta Makamashi da Sauya Muhalli (CREST) ta Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), tare da hadin gwiwar Secure Energy Project da sauran abokan habaka ci gaba da suka hada da GIFSEP, Bridge the Gap da Solar Power Nigeria.

Yayin da yake jawabi a kan taken taron, “Makamashin Hasken Rana a Najeriya: Daidaita Samun Makamashi, Samar da Kayayyaki a Gida da Sauya Fasalin Masana’antu,” Ringim ya bukaci masu tsara manufofi, ‘yan kasuwa da masana su sake nazari kan rawar da makamashi mai dorewa zai iya takawa a tsarin ci gaban Najeriya.

Ya jaddada mahimmancin dorewar manufofin gwamnati, habaka fasahohin da suka ginu a kan kwarewa da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati, jami’o’i da masana’antu domin gina abin da ya kira da “Tsarin Bunkasa Kirkire-kirkire Zuwa Kasuwa”.

Ya ce tsari zai iya sauya kayayyakin da aka kirkira a cikin gida su koma wadanda za su iya yin gogayya a kasuwannin duniya.

A cewarsa, Najeriya za ta iya koyon darussa masu mahimmanci daga sauyin tattalin arziki na kasar Indiya, wanda ya biyo bayan sauye-sauyen tsarin sassaucin ra’ayi, mayar da hannun jari ga masu zaman kansu da dunkulewar duniya da aka gabatar a shekarar 1991.

“Wadannan sauye-sauyen sun rage ikon gwamnati, sun bude kofofin tattalin arziki ga kamfanoni masu zaman kansu, gami da zuba jarin kasashen waje, sun karfafa gasa, sun saukaka samar da fasaha, sannan sun sanya kasar Indiya ta shiga cikin sahun tattalin arzikin duniya,” in ji Ringim.

Daga karshe, ya nuna jin dadinsa ga masu shirya taron saboda gayyatar da suka yi masa, sannan ya gode wa mahalarta taron bisa abin da ya bayyana a matsayin tattaunawa mai kayatarwa da amfani.

“Idan muka hada kai, za mu iya gina Najeriya inda makamashin hasken rana ba kawai zai haskaka gidajenmu da sana’o’inmu ba, zai iya tafiyar da masana’antunmu, ya baiwa mutanenmu iko, sannan ya tura kasar zuwa ga wadata mai dorewa,” in ji Ringim.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here