Hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta ƙasa FRSC ta tabbatar da mutuwar mutane 18 sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a karamar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa.
Hatsarin ya auku ne a ranar Talata a wani bangare na hanyar Dutse zuwa Kwanar Huguma.
Mai magana da yawun hukumar a jihar, kwamandan hanyoyi na rundunar, Yahaya Ibrahim, a wata sanarwa da ya fitar a Dutse, ya bayyana cewa hatsarin da ya shafi motoci kirar Volkswagen guda biyu da kuma babbar mota mai ɗaukar kaya ya samo asali ne daga gudu fiye da kima da fashewar taya da misalin karfe 12:15 na rana a kauyen Danmasara.
Hukumar ta bayyana cewa adadin mutane 20 ne hatsarin ya rutsa da su, ciki har da yara, inda 18 daga cikinsu suka rasa rayukansu a nan take.
Karanta: Mutane bakwai masu shirin zuwa ɗaurin aure sun rasu a hatsarin mota a Gombe
Direban babbar motar da kuma mataimakinsa sun tsira da raunuka daban-daban.
Jami’an ceto na hukumar sun gaggauta daukar wadanda suka jikkata da kuma gawarwakin wadanda suka mutu zuwa babban asibitin Dutse domin samun kulawar da ta dace.
Hukumar ta ce an dauki matakan gaggawa domin rage asarar rayuka a wajen hatsarin.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa wannan hatsari ya zo ne bayan wani makamancin hatsari da ya faru a ranar 25 ga watan Disamba a hanyar Ringim zuwa Sankara Beguwa a karamar hukumar Ringim, wanda aka tabbatar da mutuwar mutane 11 tare da jikkatar wasu 12.
Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya ta sake jan hankalin direbobi da masu amfani da hanyoyi da su guji gudu fiye da kima tare da tabbatar da lafiyar motocinsu, musamman tayoyi, domin kauce wa afkuwar irin wadannan mummunan hadurra a nan gaba.













































