Yadda tsohon ministan wuta ya canza akalar naira miliyan 20 daga kudin aikin Mambilla – Shaida

Saleh Mamman

 

A babbar kotun tarayya da ke Abuja, shari’ar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, ta dauki sabon salo yayin da hukumar EFCC ta gabatar da shaida cewa Naira miliyan 20 da aka ware don aikin Mambilla Hydro Power an karkatar da su don biyan kudin otal.

A yayin zaman kotun na ranar Laraba, karkashin jagorancin Mai Shari’a James Omotosho, shaidar shari’ar na uku, Kanal Adebisi Adesanya mai ritaya, ya bayyana cewa Mamman ya yi amfani da kudaden aikin don biyan hayar shekara guda a Sami Court Resort Limited, wani gidan haya da ke Abuja.

Yayin da lauya mai gabatar da kara, A.O. Mohammed, ya jagorance shi, Adesanya, wanda shi ne jami’in tsaron gidan haya kuma mai shi, ya shaida cewa an biya kudaden ne a cikin kashi-kashi da aka tura zuwa asusun UBA na gidan hayar.

Ya gabatar da “Exhibit PWC” a matsayin takardar da aka fitar wa Mamman bayan biyan Naira miliyan 20, wanda ya kama daga 30 ga Agusta, 2021, zuwa 30 ga Agusta, 2022, yana mai bayyana cewa a ranar 6 ga Satumba, 2021, Golden Bond Nigeria Limited ta biya Naira miliyan 5, sannan a ranar 23 ga Janairu, 2022, Mintedge Nigeria Limited ta biya Naira miliyan 5.

A ranar 9 ga Maris, 2022, Abdullahi Suleiman ya biya Naira miliyan 2.5, sannan a ranar 10 ga Mayu, 2022, A.I.J Global Tools Limited ta biya Naira miliyan 7.5. Adesanya ya bayyana cewa kudaden sun kasance don haya na daki guda a gidan hayae.

Mai Shari’a Omotosho ya dage shari’ar zuwa ranar 13 ga Janairu, 2025, domin ci gaba da sauraron kara. EFCC tana tuhumar Mamman da laifin hada baki da yin almundahana da kudin da ya kai Naira biliyan 33.8.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here