Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kammala komawa sabuwar hedikwatarta a Jahi, Abuja.
A yayin bikin bude sabon wurin, shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (Rtd), ya ce matakin wani bangare ne na sauya fasalin hukumar don kara inganta aikinta tun daga Janairu 2021.
Ya ce a tsohuwar hedikwatar da ke Gimbiya, Garki, ba su da isasshen wuri don aiki, hakan ya sa dole su koma sabon ginin da ke da sauye-sauye.
Marwa ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki kan goyon bayan da suka ba hukumar don cimma burinta na dakile safarar miyagun kwayoyi a kasar.
Sakataren hukumar, Shadrach Haruna, ya yaba da jagorancin Marwa wanda ya habaka yawan ma’aikata daga 5,000 zuwa 15,000 cikin shekaru uku, tare da gyaran dokokin hukumar da Majalisar Tarayya ta yi kwanan nan.
An gudanar da addu’o’in addinai biyu na Kirista da Musulunci don Shugaba Tinubu da Najeriya yayin bikin bude sabon hedikwatar.