Babbar Sallah: Mahauta a Jigawa na tunanin kara kudin yanka da gyaran Nama

Jigawa State Map 1 750x430

Wasu mahauta a Dutse, Jigawa, sun bayyana damuwarsu kan tsadar kudin sufuri, wanda zai iya shafar kudin yanka da fidar nama a lokacin bikin Babbar Sallah.

Mahautan sun ce lamarin zai yi illa ga aikin yanka da kuma samuwar aikin yanka a gida.

Wasu daga cikin mahautan sun fadi hakan ne cikin hirarrakin da suka yi daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), a ranar Alhamis a Dutse.

Binciken da NAN ta yi a Mayankar dake Dutse ya nuna cewa kudin yanka da gyaraa nama ya tashi da kusan kashi 200 idan aka kwatanta da lokacin bukukuwan da suka gabata.

Kudin yanka rago yana tsakanin Naira 5,000 zuwa sama ga kowane daya, yayin da na bijimi ke tsakanin Naira 20,000 zuwa sama, ya danganta da girman sa.

Gyaran naman, ciki har da tattarawa da gasa wa, a baya yana kai kusan Naira 5,000 ga akuya, da 10,000 ga rago ga kowane daya.

Shugaban Mahautan, Ado Sakin-Fawa, ya ce suna tsammanin farashin aikin zai hauhawa a wannan kakar saboda hauhawar kudin sufuri.

Ya ce Sallar da ta gabata an fi samun ciniki, saboda iyalai da dama sun samu karfin iya biyan kudin aikin.

“Kuɗin sufurin zuwa wurare irin su Sabuwar Kasuwa, Shuwarin da Wudil sun karu sosai a watannin baya-bayan nan.

“Sakamakon haka, mahauta da masu gyara nama yanzu suna kashe kudi da yawa wajen biyan kudin mota da sauran kudaden gudanarwa,” in ji shi.

Sarkin-Fawa ya ce mahautan da ake bawa aikin yanka a gida na iya bukatar karin kudi domin biyan kudin sufuri da ke karuwa.

Wani mahauci, Ahmad Mai Nama, ya bayyana lamarin a matsayin mara tabbas, kuma mai kalubale musamman ta fannin tattalin arziki.

Ya ce ko da yake babu kayyadadden kudin yanka da sauran ayyuka, matsin tattalin arzikin da ake ciki yanzu zai tura shi sama.

“A wannan shekara, kudin na iya dogara ne da halin tattalin arzikin da ake ciki da kudin sufuri,” in ji shi.

Ya koka cewa harkokin kasuwanci sun kasance kasa kadan gabanin lokacin bukukuwan.

Haka kuma, Babannan Abdullahi, mai gyaran nama da babbaka, ya bayyana yiyuwar kara kudin sarrafawa saboda tsadar man fetur da sauran kayan aiki.

Wani mai wajen sayar da nama, Abdullahi Awaisu, ya ce kudin aiki zai karu, sakamakon hauhawar farashin da ke samu a kasar.

Duk da haka, ya bayyana fatan cewa halin tattalin arziki zai inganta domin su more samun kasuwa mai kyau. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here