Ƙungiyar haɗin gwiwar ’yan takarar gwamna na jam’iyyun hamayya a Kano (CKSOGCF) ta sanar da shirin haɗa kai ƙarƙashin ɗan takara guda domin ƙalubalantar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna na 2027.
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a Kano, Nasiru Hassan Koguna, ne ya bayyana hakan a madadin ƙungiyar yayin taron manema labarai da ta gudanar a ranar Asabar a Kano.
Read also: Dukkan Shirye-Shiryen Yakin Neman Neman Zaben Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC, ya kammala- Lalong
Ƙungiyar ta ce ’yan takarar gwamna na jam’iyyun adawa a jihar sun sanya hannu kan yarjejeniya domin yin aiki tare wajen ceto Kano daga halin da take ciki, duk da dimbin albarkatun da take da su.
“Mun sanya hannu kan yarjejeniya ba a takarda kawai ba, har a cikin zukatanmu, a gaban Allah da kuma al’ummar Kano, cewa za mu tsaya tare, mu yi magana tare, kuma mu yi fafutuka tare,” in ji ƙungiyar.
Ta ce Kano na fama da matsalar rashin aikin yi duk da yawan matasa masu hazaka da ƙwazo, yayin da mata ’yan kasuwa a kasuwanni ke fama da ƙalubale ba tare da tallafi ba, harkar noma ke ƙara tabarbarewa, sannan asibitoci da ɗalibai ke fuskantar rashin tallafi.
Ƙungiyar ta ce Kano na da tarin albarkatun ɗan adam, kasuwanci, al’adu, addini da tarihi, amma ta rasa shugabancin da ke fifita muradun al’umma da jihar.
“Kano na da wadata, wadata a kasuwanci, al’adu, addini da tarihi, amma ta rasa shugabancin da ke sanya al’umma a gaba,” in ji ta.
Ta ce Kano ta daɗe tana gama da rarrabuwar kawuna, inda son kai da fifita muradun wasu tsirarun mutane suka mamaye muradun talakawa.
Ƙungiyar ta ce a shirye take ta fifita Kano sama da jam’iyyunta na siyasa, burinta na kai kujerar mulki da kuma muradun kowane ɗan siyasa.
Ta bayyana cewa adawa a siyasa ba laifi ba ce, kuma ba nuna ƙiyayya ba ne, sai dai fafatawa ce domin samun amincewar al’umma da kuma damar ɗaukar nauyin yi musu hidima. Ta ce wannan ne ya sa ta yanke shawarar haɗa kai domin yi wa al’ummar Kano hidima.
Read also: Rikicin APC Kano: Bangaren Shekarau sun bukaci a basu kaso 55 na tsarin shugabancin jam’iyyar
Ƙungiyar ta kuma zargi jam’iyya mai mulki da gwamnatocin da ke kan mulki a Kano da wasu jihohi da hana jam’iyyun adawa damar sanya allunan tallan siyasa da sanya kayan tallan kamfen.
“Jam’iyya mai mulki da masu riƙe da madafun iko suna hana jam’iyyun adawa a Kano da wasu jihohi damar kafa allunan tallansu da sanya kayan kamfen,” in ji ta.
“Abin da muke iya yi shi ne sanya fastoci da allunan tallanmu a wuraren da matasanmu da masu sayar da shayi suke zama, su za su iya kare su, amma jam’iyya mai mulki ta hana mu damar da Kundin Tsarin Mulki ya ba mu.”
Ƙungiyar ta ce tana da sahihan hujjoji da ke nuna cewa jam’iyya mai mulki na hana ta sanya allunan tallanta a wuraren da aka ware, yayin da ita kanta ke sanya nata kayan kamfen a wuraren.
Ta zargi waɗannan matakai da cewa ana ɗaukar su ne da gangan domin tilasta wa Najeriya komawa tsarin mulkin jam’iyya guda.
Ƙungiyar ta bayyana matakan da ake zargin ana ɗauka a matsayin haramtattu, tare da cewa sun saɓa wa Kundin Tsarin Mulki, dimokuraɗiyya da kuma ’yancin al’ummar Najeriya na zaɓar shugabanninsu.
Ƙungiyar ta ce ba ta da niyyar tunzura jama’a, tana mai cewa ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a ƙoƙarinta na gina Kano mafi kyau ga al’ummarta.
Ta kuma yi kira ga sauran jam’iyyun adawa da su shiga ƙungiyar domin haɓaka ci gaba da zaman lafiya a Jihar Kano.
Ƙungiyar ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar ɗan takarar ko jam’iyyar da za ta mara wa baya a zaɓen gwamna na 2027 ba.
Read also: Shugaban kamfe din Peter Obi ya ajiye mukaminsa
SolaceBase ta ruwaito cewa jam’iyyun siyasa 16 da suka kafa ƙungiyar sun haɗa da PRP, PDP, LP, ZLP, AAC, AA, YPP, ADP da APGA, da sauransu.













































