Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe Mai Hidimar Ƙasa

Hanging rope

Wata Babbar Kotu a Abuja ta yanke wa Jennifer Tsembe da Solomon Abuh hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe Terungwa Stephanie, mai shekaru 26, wadda ke yi wa ƙasa hidima a ƙarƙashin shirin NYSC.

Mai shari’a Kezziah Ogbonnaya ta kuma yanke wa Monday Simon hukuncin zaman gidan yari na shekaru 42 saboda rawar da ya taka a kisan.

Mai shari’ar ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin waɗanda ake tuhuma ba tare da shakku ba, ta la’akari da dukkan hujjojin da aka gabatar a gaban kotu.

Ta bayyana cewa bayanan da waɗanda ake tuhuma suka bayar da kansu sun nuna yadda Tsembe ta shirya yaudarar Stephanie, yayin da Abuh ya yi kamar mai gyaran waya, sannan suka haɗa kai wajen sace ta domin neman kuɗin fansa daga Edward Achadu, saurayin mamaciyar.

Mai shari’ar ta kuma ce Simon ma ya shiga cikin shirin, inda ya amince da taimaka wa Tsembe wajen ɗaure Stephanie tare da wani da ake kira Ja Rule, wanda har yanzu ba a kama shi ba.

Kotun ta yanke wa Tsembe da Abuh hukuncin kisa bisa laifin kisan kai, wanda sashe na 221 na Penal Code ya tanada.

Haka kuma, ta yanke wa Tsembe, Abuh da Simon hukuncin shekaru 14 a kan kowanne daga cikin laifuffukan haɗa kai wajen sace mutum, haɗa kai wajen kisan kai da kuma sace mutum, wanda ya kai jimillar shekaru 42.

Tun da farko, lauyan masu gabatar da ƙara ya bayyana cewa Tsembe, wadda kawar Stephanie ce, ta yaudare ta zuwa Maitama, Abuja, a ranar 14 ga Afrilun 2022, da nufin ba ta waya, amma daga bisani ta sace ta tare da taimakon Simon da Abuh.

Ya ce Tsembe ta zuba wani ruwa da ake zargin acid ne a fuska da jikin Stephanie.

Lauyan ya ce laifuffukan sun saɓa wa sashe na 220, 221, 272 da 274 na Penal Code, kuma ana hukunta su ƙarƙashin sashe na 221.

A yayin shari’ar, Edward Achadu, saurayin mamaciyar kuma mahaifin ɗanta, ya shaida wa kotu cewa ya taɓa yin wata alaƙa ta soyayya da Tsembe, amma ya ƙi ci gaba da ita, lamarin da ya sa Tsembe ta yi kishi da Stephanie.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here