Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, musamman Hukumar EFCC, wajen ɓata masa suna da jawo iyalinsa cikin rikicin siyasa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar da shi a ranar Juma’a, inda ya nuna damuwarsa kan abubuwan da suka faru a dangantakarsa da Gwamna Yusuf da kuma zargin amfani da hukumomin gwamnati wajen cimma muradun siyasa.
Read also: Zargin tallafawa Boko Haram: Majalisar Dattawa ta gayyaci NSA, NIA, da wasu hukumomin tsaro 2
Ya ce Gwamna Yusuf ya taɓa yi masa aiki a mukamai daban-daban, ciki har da mataimaki na musamman, babban sakataren ofishinsa da kwamishina, yana mai cewa gwamnan ya kasance ɗan takarar da ƙungiyarsu ta zaɓa a zaɓen gwamnan Kano na 2019 da 2023.
“Mai girma Abba Kabir Yusuf ya taɓa yi min aiki a mukamai daban-daban, ciki har da PA, PPS da kwamishina.
“Ya yi nasara a zaɓen 2023 ta hanyar ƙoƙarinmu na haɗin gwiwa. Dangantakarmu ta shekara 43 ce, kuma mun gina ta bisa amana,” in ji Kwankwaso.
Sai dai ya zargi gwamnan da cin amanar wannan dangantaka, yana mai cewa yana ƙoƙarin jawo shi da iyalinsa cikin ce-ce-ku-ce na jama’a domin ɓata masa suna.
Kwankwaso, wanda kuma shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya kuma zargi Gwamna Yusuf da kai ƙorafi a hukumance ga EFCC watannin da suka gabata domin a bincike shi, amma bayan ya kasa tilasta wa hukumar ɗaukar matakin da yake so, sai ya koma amfani da wata ƙungiya mai suna Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative (SACGGI).
Ya yi zargin cewa ƙungiyar ba ta da rajista a Hukumar CAC, kuma ba ta da sahihin shafin intanet ko wata alaƙa ta hukuma da EFCC ko ICPC.
“Ƙungiyar ba ta da rajista a Hukumar CAC, kuma ba ta da sahihin shafin intanet ko alaƙa ta hukuma da EFCC ko ICPC,” in ji shi.
Ya kuma zargi ƙungiyar da shirya zanga-zanga a ofishin EFCC domin matsa wa hukumar lamba, yayin da gwamnan da wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwarsa suka yi amfani da kafafen yaɗa labarai wajen gudanar da abin da ya kira kamfen na ɓata masa suna.
A cewarsa, ana zabar wasu bayanai ne a fitar da su, tare da yaɗa su ta kafafen yaɗa labarai da sauran dandamali domin nuna lamarin a mummunan yanayi.
Kwankwaso ya ce waɗannan abubuwa, waɗanda ke faruwa a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen 2027, na nuna cewa ana ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga muhimman batutuwa, raunana amincinsu da kuma rage damar da suke da ita ta samun nasara a zaɓe.
Ya kuma zargi gwamnan da faɗaɗa wannan kamfen zuwa ga sauran ‘yan takara, musamman ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Abdussalam, wanda ke ƙalubalantar wasu batutuwa da suka shafi tikitinsa a gaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotuna.
Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnan na ƙoƙarin yin tasiri a kan hukumomi, ciki har da INEC da ɓangaren shari’a, domin hana wallafa sunan Abdussalam da kuma hana shi tsayawa takara a zaɓen 2027, ta yadda Yusuf zai samu damar yin takara ba tare da abokin hamayya ba.
Read also: Wani daga cikin ministocin Tinubu ya yi murabus
Sai dai tsohon gwamnan ya yabawa EFCC bisa abin da ya kira ƙwarewa wajen gudanar da gayyata biyu da ta taɓa yi masa a lokacin da yake rike da mukaman gwamnati, yana mai cewa hukumar ta nuna taka-tsantsan da kare mutuncin aikinta.
Kwankwaso ya ce ya ci gaba da kasancewa da tsaftataccen tarihi na fiye da shekaru 11 bayan barin gwamnatin Kano, bayan ya yi wa’adin mulki biyu na shekaru takwas, baya ga shekaru 17 da ya yi a aikin gwamnati.
“Na ci gaba da kasancewa da tsaftataccen tarihi fiye da shekaru 11 bayan barin gwamnatin Kano, bayan na yi wa’adin mulki biyu na shekaru takwas, baya ga shekaru 17 da na yi a aikin gwamnati.”
Ya kuma bayyana wasu mukamai da ya riƙe a baya, ciki har da mataimakin shugaban majalisar wakilai a lokacin Jamhuriya ta Uku da ta rushe, wakilin da aka zaɓa zuwa taron tsara kundin tsarin mulki na 1994–1995, Ministan Tsaro, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan Darfur, wakilin Arewa maso Yamma a Hukumar NDDC da kuma sanata a majalisar dattawa ta takwas.
Kwankwaso ya yi kira ga masu rike da mukaman gwamnati da matasa ‘yan siyasa da su yi taka-tsantsan, yana mai gargaɗin cewa mukaman gwamnati na wucin gadi ne, don haka ya kamata masu mulki su riƙa lura da ayyukansu.
Ya kuma gode wa jama’a da suka ƙi yarda a yaudare su, tare da ci gaba da kare mutuncinsa da tarihin ayyukansa.
Ya yi kira ga ‘yan siyasa da su mutunta ‘yancin hukumomi, tare da guje wa duk wani abu da zai iya raunana amincinsu ko rage yarda da jama’a a kansu.
Sai dai kuma, Gwamna Abba Yusuf ya musanta zargin
Da yake mayar da martani kan zarge-zargen, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya musanta zargin a wata tattaunawa da SolaceBase ta yi da shi a ranar Juma’a.
Bature ya ce gwamnatin jihar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ba su da wata matsala da Kwankwaso da za ta sa su kai shi gaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ya ce tsohon gwamnan ya shafe shekaru 11 yana wasan buya da EFCC, saboda wasu zarge-zarge, ciki har da na cire Naira miliyan 70 daga kowace ƙaramar hukumar Kano, wanda idan aka haɗa ƙananan hukumomi 44, ya kai sama da Naira biliyan uku, wanda aka rubuta ƙorafi ga EFCC.
“Ko kuwa batun kuɗin fansho na shekarar 2016 ne, wanda yake a fili kuma kowa ya san da shi?” in ji shi yana tambaya.
Kwamishinan ya ce idan gwamnatin jihar tana da wani abu a kan Kwankwaso, da hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ko ma’aikatar shari’a za su kai shi kotu.
Read also: Lasisin tace Mai aka bai wa Dangote ba na Sifurinsa ba- Dallalan Mai
Ya bayyana zarge-zargen a matsayin ƙoƙarin neman tausayin jama’a da kuma yin amfani da dabarar nuna kansa a matsayin wanda aka zalunta.













































