Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana sunayen mambobin kwamitin da ta kafa domin binciken zargin cin zarafin jima’i da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar.
Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Dr Bala Salisu Zango, ya fitar ranar Alhamis.
Read also: Wike ya bai wa masu karya dokar amfani da filaye wa’adin kwanaki 14 su biya tara
Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da naɗin mutum tara da za su kasance mambobin kwamitin, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Amiru Sanusi mai ritaya.
Sauran mambobin sun haɗa da Mai ba gwamna shawara kan harkokin masarautu, Usman Abba, mai shari’a Sadiq A. Mahuta mai ritaya, Galadiman Katsina, Kwamishinan Harkokin Addini, Isah Dabai da Alhaji Lawal Aliyu Daura.
Haka kuma, an naɗa Farfesa Halima Kabir ta Sashen Harsuna da Al’adu na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Dr Bala Salisu Zango, Hajiya Khadija Abdulkadir, mai ba Masarautar Belgium shawara kan diflomasiyyar tattalin arziki da Babbar Lauya kuma Kwamishinar Shari’a ta jihar, Fadila Muhammad Dikko, wadda za ta kasance sakatariyar kwamitin.
Sanarwar ta ce an ɗora wa kwamitin alhakin gudanar da bincike kan zargin, gayyatar duk waɗanda suke da alaƙa da lamarin da kuma gano dalilin ziyarar matar baƙuwar yawon buɗe ido zuwa fadar sarkin.
Read also: Gwamnatin jigawa ta kaddamar da Kwamitoci dan samar tallafi ga wadanda ambaliya ta shafa
Haka kuma, kwamitin zai duba takardu, bayanai da sauran hujjoji da suka shafi lamarin, domin tantance irin rawar da sarkin ya taka tare da bayar da shawarwarin matakan ladabtarwa ko gyara da suka dace.
Sai dai ana sa ran kwamitin zai miƙa rahotonsa ga gwamnatin jihar cikin makonni huɗu daga ranar ƙaddamar da shi, kuma zai fara aiki nan da nan bayan ƙaddamarwa.
Sanarwar ta buƙaci al’umma da su baiwa kwamitin damar gudanar da bincikensa cikin ’yanci ba tare da matsin lamba ba.
Haka kuma, gwamnatin ta yi gargaɗi kan kauce wa kalamai ko ayyukan da ka iya kawo cikas ga binciken, tare da tabbatar da cewa za a yi adalci bisa sakamakon binciken kwamitin.
SolaceBase ta ruwaito cewa wata mata baƙuwar yawon buɗe ido ta zargi sarkin da cin zarafinta ta hanyar lalata lokacin da ta ziyarci fadarsa a mako na biyu na watan Nuwamba.
Read also: AC Milan na dab da lashe gasar Serea A ta kasar Italiya
Bayan zargin ya janyo ce-ce-ku-ce, gwamnatin jihar ta dakatar da harkokin gudanarwa da zirga-zirgar sarkin a hukumance, tare da kafa kwamitin bincike kan lamarin.













































