Fursunoni 3 sun mutu yayin yunkurin tserewa daga gidan yari a Kwara – NCoS

Ilorin custodial centre (1)

Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Kasa (NCoS) ta ce fursunoni uku sun mutu yayin yunkurin tserewa daga gidan gyaran hali da ke Oketura, Old Ilorin a Jihar Kwara.

A ranar 18 ga Nuwamba, fursunoni biyu da aka yanke wa hukuncin kisa sun tsere daga gidan yarin, bayan da ake zargin sun fasa katanga tare da bi ta kanta.

Bayan faruwar lamarin, rundunar NCoS ta Jihar Kwara ta fitar da sunayen fursunonin da suka tsere tare da hotunansu.

Hukumar ta bayyana sunayen wadanda suka tseren din da Segun Abraham Nasiru da Oluwasegun Omoyajowo Ajiboye.

Da yake magana yayin ziyarar da ya kai Ilorin a ranar Laraba, Babban Kwanturola Janar na NCoS, Sylvester Nwakuche, ya ce fursunoni bakwai ne suka yi yunkurin tserewa daga gidan yarin, amma jami’an gidan yarin suka dakile yunkurin.

Nwakuche ya ce jami’an sun hana fursunoni biyar tserewa, yayin da biyu suka yi nasarar tserewa.

Ya kara da cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji Ojo, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

“Abin takaici, an sanar da mu cewa uku daga cikin fursunoni biyar da ba su samu tserewa ba sun rasa rayukansu. Wannan lamari ne mai matukar ban tausayi,” in ji shi.

Ya ce an kafa kwamitin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, inda ya kara da cewa duk wanda aka samu da hannu a ciki zai fuskanci hukuncin da ya dace na doka.

“Dole ne mu gudanar da bincike kan wannan lamari ta hanyar gwajin likita da kuma tattara bayanan sirri,” in ji shi.

Babban jami’in ya ce an gina gidan gyaran hali na Oketura ne tun zamanin mulkin mallaka, kuma a halin yanzu yana fama da cunkoso.

Ya bayyana cewa sama da fursunoni 4,000 ne ke jiran hukuncin kisa a gidajen yari daban-daban na Najeriya.

Nwakuche ya bukaci gwamnonin jihohi da su sauya hukuncin kisa zuwa daurin rai-da-rai, idan ba za su iya sanya hannu kan takardun aiwatar da hukuncin kisa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here