Akpabio ne zai zama sabon shugaban majalisar dattijai – Ganduje

Godswill Akpabio 1 727x430 1
Godswill Akpabio 1 727x430 1
Gandujen ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wajan wani taro da yai da gwamnan jir  Cross River a Calabar.
Shugaban fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari, na daya daga cikin wadanda suka halarci taron.
Gambari da Ganduje sun je Cross River ne domin halaratar taron nada sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a matsayin Uban jami’ar Calabar, “University of Calabar”.
Ganduje ya ce zabar Akpabio abu ne wanda an riga tuni an gama shiryashi, sai dai kuma bai bayyana yanke wukuncin ko na da alaka da jami’iyyar APC ba.
Gandujan ya katra da cewa, Akapbio yana da kwarewar da zai iya hada kan yan Najeriya idon ya zama shugaban majalisar.

 

 

“Ina tabbatar muku da cewa zai zama, kawai mu jira lokaci ” Inji shi.

Ya yin da yake jawabi a gurin taro, gwamna Ben Ayade ya bayyana farincikin sa bisa kudirin su Ganduje na zabar Akapbio.

“Ina mutukar gode muku bisa yunkurin kawo kujerar shugan majalisar dattijai Kudu maso Kudu, sanan kuma aka bawa danuwanmu daga makociyar jihata wanan mukami.”

“Mun kara godemuku bisa bamu damar cika burinmu na yin tashar ruwa ta Bakassi seaport.”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here