Gwamnatin Jihar Kano, hadin gwiwar da Tarayyar Turai (EU) da kuma Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) sun fara tsara shirin ilimi na shekaru 10.
Shirin ya kunshi tsarin aiki na shekaru 3 domin magance matsalar koyo a jihar.
Shirin wanda aka sanya wa suna “2026–2035 Kano State Strategic Education Sector and Operational Plan SESP & SESOP”, wanda ke da manufarrage yawan yaran da ke daina zuwa makaranta, inganta harkar koyo, da sauya fannin ilimin jihar gaba daya.
Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Karanveer Singh, ya ce tsare-tsaren suna da matukar muhimmanci wajen magance matsalar yara dake barin makaranta da inganta samun ilimi mai inganci a jihar.
Singh ya ce ilimi shine ginshikin cigaban kasa, saboda haka ya zama dole a tallafawa gwamnatin jihar da ta tarayya a wannan fanni.
“Ilimin yara abu ne mai matukar muhimmanci idan muna son kasar nan ta cigaba. A Najeriya, muna da yawan yaran da ke barin makaranta, don haka dole ne mu dawo da wadannan yara makaranta.
A cewarsa UNICEF ta hada kai da Ma’aikatar Ilimi, SUBEB, da sauran masu ruwa da tsaki wajen gina wa da taimaka musu don samun ingantaccen ilimi.
A nasa bangaren, mai baiwa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf shawara na musamman kan gyara da bunkasa harkokin ilimi a jihar, Haladu Mohammed, ya sake jaddada kudurin gwamnati na kawo sauyi da gyara a fannin ilimin jihar.
Ya ce kokarin gwamnatin a bayyana ne yake, duba da irin tallafin da ta zuba a fannin na ilimi da kuma ayyana dokar ta baci a fannin tun da suka hau mulki.
Masaniya daga Cibiyar Kasa ta Shirye-Shiryen Ilimi da Gudanarwa NIEPA, Dr Lara Ogunsola ta ce cibiyar ta hada kai da UNICEF wajen ba da tallafin fasaha ga shirin.
Ta tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa shirin ba zai kasance kawai a takarda ba, sai dai zai zama mai yiwuwa, kuma mai dorewa.
A nasa bangaren, guda cikin shugabannin inuwar tabbatar da nagartaccen Ilimi ta Kano (K-SAFE), Dr Auwalu Halilu ya ce kungiyoyin jama’a suna ba da gudummawar ra’ayoyin al’umma domin tabbatar da shirin ya magance kalubalen da ke fuskantar fannin ilimi a fadin jihar yadda ya dace.












































