Ba a Bukatar Yin Gwajin Korona Ga Matafiya – Gwamnatin tarayya

PASSENGERS
PASSENGERS

Gwamnatin tarayya ta ce daga Yanzu ba buƙatar yin gwajin cutar kwalora ga matafiya”

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya ta rubuta mai kwanan wata 12 ga watan Disamba, 2022, kuma ta aikewa da kamfanonin jiragen sama.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, wasikar Mai dauke da sa hannun daraktan hukumar Musa Nuhu.

Wasikar ta ce: “Gwajin balaguron cutar COVID-19: Ba a buƙatar yin gwajin COVID-19 kafin tafiya da kuma bayan isowa ga duk fasinjoji. An dakatar da gwaje-gwajen PCR da ake buƙata ga duk fasinjojin da ba su da cikakken alurar rigakafin.

Hakan kuma, ban da dakatar da gwaje-gwajen COVID, Daga yanzu sanya abin rufe baki shima bai zama dole ba ga fasinjojin da ke cikin jirgin sama.

“Sanya abin rufe fuska a cikin tashar jirgin sama da kuma ma’aikatan filin jirgin sama, fasinjoji da ma’aikatan jirgin bai zama dole ba.

“Kiyaye nisantar jama’a a tashar jiragen sama shima bai zama dole ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here