Shugaban cibiyar dake horar da akantoci ta kasa reshan jihar Kano ICAN, Malam Salisu Haruna, ya ce cibiyar zata bada horo kyauta a jihar Kano ga daliban da suka kammala karatun sakandare dama wadan da suka kammala Jami’o’i.
Ya ce horon zai bawa mutanan kano dama su zamu akantoci domin cigaba da bawa dukiyar al-uma kariya da kuma habbaka tattalin arzikin jihar Kano da kuma kasa baki daya.
Shugaban cibiyar ya bayyana aniyar cibiyar na bada horon ne a taron manema labarai da cibiya ta shirya ranar Talata a jihar Kano, domin sanar da al-umma amfanin da cibiyar take dashi, gudun mawar data ke bayarwa da kuma sanar da jama’a gangamin taron da cibiyar zata fara gudanar daga ranar 19 zuwa 22 ga watan Disamba domin murnar cikar cibiyar shekara 50 da kafuwa.
Bakin murnar cikar cibiyar shekara 50, zai hada da ziyara, kaddamar da mijalla, taron liyafa tare da bada shidodin giramawa da sauran shagalilika.
“Daga shekarar 2019 zuwa yau cibiyar ICAN ta sami tarun nasaruri wajan tsarin bawa mutane horo, sakamakon kokari da kuma jajircewa na membobin cibiyar tare da masu ruwa da tsaki dakuma jajircewa ta tsohon shugaban cibiyar Dakta Abubakar Umar Farouk.
“Tun daga lokacin da muka fara shirya jarrabawa ta cibiyar ICAN, muke samin yabo dangane ga ingancin da jarrabawar take dashi dakuma ingancin daliban da aka yayewa.”
Da yake jawabi a wajan taron manema labaran, tsohon shugaban cibiyar, Dakta Abubakar Umar Farouk, ya ce cibiyar na bada tarin gudun mawa wajan kula da shigar da fitar kudi domin bawa masu ajiya kariya ba tare da cuta ba.
Ya kuma ja hankalin iyaye dasu kawo ‘ya ‘yan su domin cibiyar ta basu horo wanda yake kauta ne batare da an biya ko sisi ba.