Ramadan: ‘Yan kasuwa a jihar Kano sun koka kan karancin ciniki

'Yan kasuwa, koka, karancin, ciniki, ramadan, azumi
Yayin da watan azumin Ramadan mai alfarma da albarka ya fara, ‘yan kasuwa a jihar Kano sun ci gaba da kokawa kan rashin zirga-zirgar kwastomomi...

Yayin da watan azumin Ramadan mai alfarma da albarka ya fara, ‘yan kasuwa a jihar Kano sun ci gaba da kokawa kan rashin zirga-zirgar kwastomomi.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwa da suka zanta da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, sun danganta lamarin da karancin shigowar kwastomomi kasuwanni.

Wani dillalin kayan abinci, Malam Tanko Idris, ya ce idan aka kwatanta da shekarun baya, tallace-tallace ya ragu a bana.

Karin labari: Burtaniya za ta kashe £117m don ba da kariya ga musulmai

Idris ya lura cewa duk da cewa farashin wasu kayayyaki, musamman kayan masarufi ya kan yi zafi a lokacin azumin watan Ramadan, amma har yanzu mutane na sayen kayayyaki.

Shi ma wani dillalin kayayyakin, Saminu Dauda, ​​ya koka da yadda harkokin kasuwanci ke kara tabarbarewa, ya bayyana cewa tabarbarewar tattalin arzikin kasar ya taimaka wajen haifar da mummunan yanayi.

Wani mai sayar da kayan lambu, Sani Ali, ya koka da cewa lamarin ya bada mamaki idan aka kwatanta da abin da yake gani a kasuwa a duk lokacin da watan Ramadan ke gabatowa.

Karin labari: Hamas ta bar wurin da ake tattaunawa a Gaza

Ali ya ce kwastomomi da dama sun koka da karancin kudade saboda yanayin tattalin arziki.

Ya kuma koka da yadda yanayin tattalin arziki ya shafi karfin saye na kwastomomi da dama.

Wani mai saye Nura Baba ya koka da tsadar shinkafa da gero da fulawa da kuma sikari, wanda a cewarsa yana damun sa yayin da lokacin azumi ke gabatowa.

Karin labari: Anga watan Ramadana a Najeriya – Sarkin Musulmi

“Misali, ana siyar da sukari sama da Naira 5,5000 kan kowacce mudu, shinkafar da ake sayar da ita sama da Naira 3,500, gero ana sayar da shi akan Naira 1,800 sai kuma kiretin kwai kan Naira 3,300 ta yaya suke so mu ci abinci a cikin watan Ramadan?” in ji Nura.

Ya kuma yi kira ga dillalai da dillalan kayan abinci a jihar da su rage farashin su a cikin watan mai alfarma na azumin Ramadan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here