Majalisar wakilan kasar nan ta dage ci gaba da zamanta zuwa ranar 30 ga watan Janairun shekarar da muke ciki ta 2024.
Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da bulaliyar majalisar, Yahaya Danzaria ya aikewa daukacin ‘yan majalisar, inda ya ce za a koma zaman majalisar ne a ranar 30 ga watan Janairu.
Karanta wannan: Gwamna Abba ya nada Ganduje a matsayin mamba na majalisar dattawan Kano
Hakan na zuwa ne makonni biyu da zartar da kasafin kudin shekarar 2024 na Naira tiriliyan 28 da doriya.
Tun da farko dai ‘yan majalisar sun tsayar da ranar 23 ga watan Janairu a matsayin ranar koma wa domin ci gaba da zaman majalisar.
Karanta wannan: Gwamnatin Najeriya ta wofintar da mu a Sudan-Wasu Dalibai
Sakon ya ce “An umarce ni da in sanar da Mambobin majalisar wakilai cewa an dage ranar koma wa zaman majalisar dattawa da ta wakilai zuwa ranar Talata 30 ga watan Janairun 2024 da karfe 11:00 na safe.’’












































