Gwamna Abba ya nada Ganduje a matsayin mamba na majalisar dattawan Kano 

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano

Gwamnatin jihar Kano ta kafa majalissar dattijan jihar Kano domin karbar shawarwari don ciyar da Al’umma gaba.

Gwamna Abba Kabir ne ya bayyana haka a zantawar sa da manema labarai ranar Asabar a Abuja.

Karanta wannan: Kotun koli ta tabbatar da Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan Zamfara

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wadanda za su kasance mambobin majalissar sun haɗar da tsoffin gwamnoni jihar, mataimakan gwamnoni, tsoffin shugabanin majalissar dokokin jiha, da tsoffin alkalai da ƴan kasuwa ‘yan asalin jihar nan bayan tantance su.

Ya kara da cewa yanzu haka a cikin mambobin majalissar dattawan Kanon ya sanya, Rabiu Musa Kwankwaso, da Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Malam Ibrahim Shekarau.

Kazalika yace gwamnatin sa tana maraba da shawarwarin al’umma domin ciyar da Jihar Kano gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here