Kungiyar dake tallafawa Mata manoma ta Najeriya (WOFAN) ta bayyana zaman lafiya tare da mutunta juna a tsakanin manoma da makiyaya a matsayin wani mataki na inganta wadatar abinci a Najeriya.
Shugabar kungiyar, Dakta Salamatu Garba ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da ta yi da jaridar SolaceBase, a yayin wani taron bada horo na kwanaki 5 na kasa da kasa kan bunkasa kasuwanci: sadarwa mai inganci, da aka gabatar a birnin Doha na kasar Qatar wanda Prospect Development Services da WOFAN-ICON2 bisa tallafin gidauniyar Mastercard suka shirya.
Dr. Salamatu Garba ta ce ana iya magance rigingimun da ake ci gaba da samu tsakanin manoma da makiyaya wanda galibi ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyi ta hanyar sadarwa mai inganci kan zabin kalmomin da suka dace a dinga kira ko banbance manoma da makiyaya.
“Lokacin da aka nadi ni a matsayin Jakadiyar Zaman Lafiya Ta Majalisar Dinkin Duniya shekaru biyu da suka wuce, na yi alkawarin bayar da gudummawa ta wajen wanzar da zaman lafiya ta hanyar gina al’umma
“Daya daga cikin abubuwan da muka koya a Doha shi ne cewa ko sunan da ake kiran manoman dabbobi “Makiyaya” bai kamata ba, kamata ya yi kamar yadda muke kiran manoma, kamar manoman gyada ko waken soya, ko kuma manoman shinkafa, me zai hana suma makiyaya a dinga kiransu manoman dabbobi?”
“Lokacin da aka riga aka yi musu lakabi da makiyaya, ko kuma a bayyana su a matsayin Fulani makiyaya, yaya kuma za’a kira Yarabawa, Hausawa ko inyamurai da suke kiyo?”
Dr. Salamatu Garba ta kara da cewa ”Bari mu fara daga nan, manoman amfanin gona da masu kiwon dabbobi su yi aiki tare a matsayin abokan hadin gwiwa, don haka mu koma gida mu fara fadakarkawa tare da wayar musu da kai a kan wadannan matsalolin, kuma muna buƙatar hadin gwiwa da kafofin watsa labarai domin gudanar da aikin don samun nasara”
‘’ A lokacin da muka fara ganin juna cikin girmamawa da mutuntawa, an riga an magance rabin matsalar, domin duk mafiya yawan matsalolin na farawa daga kalaman baki, ɗabi’a da abin da muke faɗa wa juna.”
Shima da yake jawabi a yayin taron bada horon, Dr Nahemiah Danbaba na Cibiyar Binciken hatsi ta kasa, Badegi, ya ce bibiyar ma’ana da manufar noma, fasaha ce da kimiyyar kiwon dabbobi da noman amfanin gona don dorewar abinci mai gina jiki ga mutum da dabbobi.
A cewarsa, idan aka yi la’akari da wannan ma’anar, ana nufin noma yana da bangarori biyu musamman, mutanen da ke aikin noman amfanin gona da kuma kiwon dabbobi.
‘’Saboda haka idan muka kuduri aniyar bunkasa fannin noma, akwai bukatar a kalli noma ta bangarori biyu masu muhimmanci, akwai wadanda ke da hannu wajen kiwon dabbobi, wanda shi ne babban tushe, da kuma mutanen da ke da ruwa da tsaki wajen samar da amfanin gona, inda muke samun sinadarin carbon hydrate da sauran nau’o’in abinci mai gina jiki.
Ya ce, manoman dabbobi sun dade ba sa samun kulawar da ya kamata idan aka kwatanta da manoman amfanin gona tsawon shekaru.
‘’Sai kuma a duba bukatar da kowanne ke so, a duk shekara akwai kasafin kudin tallafa wa manoman shinkafa, da manoman masara, amma da kyar ka ji an tallafa wa manoman dabbobi, sai dai kila masu kiwon kaji wadanda ba su kadai ba ne a cikin tsarin kiwon na dabbobi.
‘’Idan muka kalli wannan da abin da cibiyarmu ke yi a matsayin wani bangare na aikinmu, za mu duba cewa abinda yafi kyau ga wadannan kungiyoyi biyu shi ne su zauna tare da bayar da gudunmawarsu ga ci gaban kasa.
”Haka zalika muna duban yadda za su iya ba da gudummawa ga dorewar muhalli, ci gaban matasa da mata da kuma tasiri kan abinci mai gina jiki duk waɗannan batutuwa ne da muke yi a matsayin ƙungiya don tallafawa mafi yawan ayyukanmu.
“Don haka yin aiki da kungiyar WOFAN dake da kwarewa wajen yin aiki da kananan manoma, musamman ma masu karamin karfi, cibiyar tana hada kai da wannan kungiya domin baiwa manoman tallafin da suke bukata domin su zauna tare da tallafa wa junansu, don inganta rayuwarsu.”
Taron horaswar ya samu halartar jami’an kungiyar WOFAN daga jihohin Bauchi, Kaduna, Kano, Abuja, Benue, da kuma masana harkar noma daga cibiyar binciken hatsi ta kasa, Badegi, National Agricultural Extension and Research Liaison Services (NAERLS) Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, da shugabannin gidajen yada labarai na SolaceBase da Express Radio tare da wasu yan kasashen waje 6 da suka hada da Tunisia, Lebanon da Ghana da dai sauransu suka samu damar halarta.