Tsohon kwamishinan yada Labarai na tarayya kuma shugaban Kudu-maso-Kudu, Edwin Clark, ya mutu.
Shugaban kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF) ya rasu yana da shekaru 97 a daren ranar Litinin, kamar yadda wata sanarwa da Farfesa C. C. Clark ya sanya wa hannu a madadin iyalansa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Iyalan Clark-Fuludu Bekederemo na Garin Kiagbodo na jihar Delta.
Chief (Dr.) Sanata Edwin Kiagbodo Clark OFR, CON an sanar da mutuwar sa a ranar Litinin 17 ga Fabrairun 2025.
Iyalin nasa za su sanar da sauran bayanai daga baya.
Karin bayani……