Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Hon. Blessing Agbebaku ya dakatar da wasu ‘yan majalisar guda uku bisa zargin yunkurin tsige shi da wasu mambobin majalisar manyan jami’an (POC).
‘Yan majalisar da aka dakatar sune Hon. Donald Okogbe (PDP Akoko-Edo II), da Bright Iyamu (PDP Orihonmwon South), da kuma Adeh Isibor (PDP Esan North East I).
Karin labari: Najeriya za ta rage lantarkin da ta ke bai wa Nijar da Benin da Togo
A ranar Litinin din da ta gabata ne Agbebaku ya yi zargin a zaman majalisar cewa ‘yan majalisar uku da aka dakatar na da alaka da wasu dakaru daga waje wajen kawo hargitsi tare da tsige shugabannin majalisar.
Ya kara da cewa wasu mutane sun shigo da likitocin asali a harabar majalisar da tsakar daren ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, 2024, don yin tsafi da barin laya.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Gobara ta tashi a gidan tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau
‘Yan majalisar da aka dakatar, yayin da suke mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi musu a zaman da suka yi da juna, sun yi ihu cewa, “Mai girma shugaban majalisar, ba ka da hurumin dakatar da wani mamba (’yan majalisar) baki daya.”