Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya amince da Naira miliyan dubu 1 don tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin Ahoada ta yamma da Ogba/Egbema dakuma Ndoni na jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin labarai Mista Kelvin, ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Fatakwal.
Wike ya kuma kafa wata runduna mai karfin gaske kan yadda za a raba kayan agajin ga al’ummomin da abin ya shafa.
Ya ce an bayar da tallafin ne domin baiwa iyalai marasa galihu, musamman a yankunan Ahoada dake kananan hukumomin biyu, yankunan da suka fi fama da bala’in ambaliyar ruwan a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa ambaliyar ta mamaye gidaje da filayen noma tare da tilastawa mazauna yankunan da abin ya shafa yin kaura zuwa wasu wurare.
Babban sakatare na ofishin kula da ayyuka na musamman, ofishin sakataren gwamnatin jihar, Dokta George Nwaeke ne zai yi aikin a matsayin shugaban kwamitin, yayin da Uwargida Inime Aguma za ta kasance Sakatariya.
Wike ya bayyana sunayen sauran mambobin kwamitin a matsayin shugaban karamar hukumar Ahoada ta Yamma, Hope Ikiriko; shugaban karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, Vincent Job; da Daraktan Gudanarwa, Ma’aikatar Ayyuka na Musamman Chukwuemeka Onowu.
Gwamnan ya ce dukkanin mambobin kwamitin za su gana da shi a gidan gwamnati da ke Fatakwal ranar Alhamis.













































