Dan majalisa a Kano zai baiwa mata da matasa horon kiwon kaji tareda ba su tallafi

IMG 20221012 WA0426
IMG 20221012 WA0426

Awani bangare na kokarin kawar da fatara da talauci dake ciwa mata da matasa tuwo a kwarya, dan majalisar wakilai mai wakiltar Tarauni a majalisar kasa Honarabul Hafiz Kawu Ibrahim OON ya shirya taron bita na yini biyu dan bada horon kiwon kaji ga mutane sama da 100 a mazabarsa. .

Cikin wata sanarwa da mai taimakawa dan majalisar na musamman kan harkokin labarai, Bashir Suwaid ya fitar, ya ce fom ns karbar horon kyauta ne a ofishin mazabar Hafiz Kawu Ibrahim da ke farm center dab da gidan sinima na Marhaba a Kano.

Ya ce ana cigaba karbar fom din izuwa yanzu kuma ana saran rufewa a ranar Alhamis, 13 gawatan Oktoba 2022.

A cewar sanarwar, wadanda suka ci gajiyar horon bayan kammala horon za a ba su abubuwa da dama da suka hada da, tallafin tsabar kudi naira Dubu 50 da abincin kaji kala kala me nauyin kilo 25, da abubuwa da dama an musu tanadi.

Sanarwar ta kara da cewa, horon na kwana biyu kan kiwon kaji zai fara ne a ranar Juma’a kuma za a kare ranar Asabar mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here