Za mu baiwa Kwankwaso masauki idan ya yanke shawarar shigowa cikin mu, yana bukatar matsuguni, za mu samar masa – Ganduje

GandujeKwankwso 750x430

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Dr Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyyar za ta bai wa tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso masauki idan ya yanke shawarar shiga cikin ta.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ya karbi bakuncin Alhaji Yusuf Ata, karamin ministan gidaje da raya birane, Ganduje ya ce: “Jam’iyyar APC na kara zurfafa da fadada dimokuradiyya a kasar nan.

“Kwankwaso kifi ne daga ruwa, yana kokarin neman hanyar komawa cikin ruwa.

“Ba za mu so mu bar shi gaba daya a yashe ba, har yanzu muna iya shigar da shi cikin mu idan yana son shiga”.

Karin karatu: Cikin Hotuna: Ganduje ya karbi bakuncin Kawu Sumaila, Rurum, Baffa Bichi, Sha’aban Sharada, Diggol a matsayin sabbin ‘yan APC

Tun da farko, Ata, wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano ne ya ce ya ziyarci Ganduje ne domin ya girmama shi da kuma nuna goyon bayansa ga abin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi wa jihar Kano.

“Muna goyon bayan Tinubu kuma muna aiki ba dare ba rana don ganin mun kwato jihar Kano a 2027,” in ji shi.

Da yake magana kan harkar ‘Kwankwasiyya’, Ata ya ce zamanin kwankwasiyya na dab da zama tarihi a jihar.

“A gare ni, ba zan so a yi wa tsohon gwamnan jihar Kano tarba a jam’iyyar APC ba, amma ba ni da zabi idan shugabanmu na kasa ya yanke shawarar sanya shi a cikin jam’iyyar.” A cewar Ata.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here