Gwamnan Kano ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiya kafin Aure

Gwamnan, Kano, Abba, Kabir, Yusuf, tantance, lafiya, aure, rattaba, hannu
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son...

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son aure.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce dokar tana ganin ya zama dole domin rage yiwuwar haihuwar yara masu wasu matsalolin kiwon lafiya kamar irinsu sikila da cutar kanjamau da kuma ciwon hanta.

“Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure ba a Kano ba tare da ba da takardar shaidar tantance lafiyar jinsin halitta, hepatitis B da HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaka da su ba.

Karin labari: UTME: JAMB ta fitar da karin sakamakon masu yin jarrabawa 531

“Wannan shiri ya yi daidai da kudurin gwamnan jihar Kano na inganta da samar da yanayi mai kyau ga bangaren kiwon lafiya, da nufin ganin Kano ta kubuta daga matsalolin kiwon lafiya ko kuma rage radadi.

“Dokar ta wajabta yin gwajin cutar kanjamau da Hepatitis da genotype da sauran gwaje-gwajen da suka dace kafin aure. Har ila yau, ta haramta duk wani wariya ko kyama ga mutanen da ke dauke da kwayar cutar HIV/AIDS, dadai nau’ikan cututtuka.”

Karin labari: Naira ta kara daraja a kasuwar canjin kudade

Gwamna Yusuf ya kuma jaddada cewa manufar aiwatar da dokar ita ce tabbatar da tsarkin aure a jihar Kano da kuma tabbatar da haihuwar ‘ya’ya masu lafiya, ba tare da wata cuta da za a iya magance ta ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Dokar ta bayyana cewa duk mutumin da aka samu da laifin sabawa tanadin ta, ya aikata laifi kuma idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar tarar Naira dubu dari biyar, da wasu shekaru ko kuma duka biyun.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here