A ranar Talata ne mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ‘yan majalisar masarautar Kano suka kaiwa tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ziyarar ta’aziyya a gidansa da ke Kano.
Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa gobara ta kone gidan Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau a daren ranar Lahadi.
Karin labari: Gwamnan Kano ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiya kafin Aure
An ce gobarar ta yi barna sosai a gidan musamman bangaren tsohuwar matarsa ta uku Hajiya Halima da matarsa ta hudu Farfesa Gaji Fatima Dantata.
Daga cikin wadanda suka fara jajantawa iyalan a ranar Litinin, akwai dattijon jihar kuma hamshakin attajirin nan, Alhaji Aminu Dantata.