YANZU-YANZU: Ganduje ya kai wa Kwankwaso ziyarar ja’aziyyar kaninsa

79CAE24D CCF8 4B31 AA78 C8A6E6C76A63
79CAE24D CCF8 4B31 AA78 C8A6E6C76A63

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa tsohon gwamna kuma tsohon Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ziyarar ta’aziyya bisa rasuwar kanin sa Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso.

Gwamna Ganduje ya kai ziyarar a gidan Kwankwaso dake Millar Road a cikin birnin Kano.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Inuwa Kwankwaso ya rasu ne jiya litinin a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan ya sha fama da jinya, yana da shekaru 64.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da rikicin siyasar Kano ke kara kamari, inda ake zargin Gwamna Ganduje zai koma ya sake hadewa da tsohon mai gidan sa Kwankwaso.

Sai dai a Watan Disamban shekarar 2020 ne mahaifin Sanata Kwankwaso ya rasu, amma gwamna Ganduje bai kai masa ziyarar ta’aziyya ba, wanda masana suka alakanta hakan da rigimar siyasa da suke yi a wannan lokacin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here