Gobara ta lalata sama da shaguna 300 a Sokoto

176C59AB 029E 4450 94D5 510A4986E201
176C59AB 029E 4450 94D5 510A4986E201

A kalla sama da shaguna 300 ne suka lalace a wata gobara da ta tashi a kasuwar Kara dake babban birnin jihar Sokoto.

A cewar shaidun gani da ido gobarar ta tashi ne da misalin karfe hudu na asubahin yau Talata.

Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Akwai bayanai mabanbantan bayanai kan musabbabin tashin gobarar.

Yayin da wani ya ce gobarar ta tashi ne a kusa da sashin hatsi kafin ta zarce zuwa wasu sassan kasuwar, wani kuma ya ce gobarar ta tashi ne daga bangaren maƙeran karfe.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da abin ya shafa, Jamilu Isa, ya ce ya yi asarar duk yakin da ya yi da wutar.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Sokoto, Alhaji Chika Sarkin Gishiri, ya ce gobarar ta lalata kayayyakin da suka kai na miliyoyin naira.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa ta hanyar ba su tallafin kudi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here