Majalisar dattawa ta tabbatar da Mu’azu Sambo a matsayin minista

516CCFC0 92D5 493B 9A36 764FE8AA39C1
516CCFC0 92D5 493B 9A36 764FE8AA39C1

Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Mu’azu Sambo daga Taraba a matsayin minista kuma mamba a majalisar zartarwa ta tarayya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya tabbatar da  Sambo bayan an  tantance shi a zauren majalisar a ranar Talata.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya aikewa majalisar sunan Muazu Sambo yana naiman ta amince masa ya nada shi minista kuma mamba a majalisar zartaswa ta kasa.

A yayin tantancewar, Sambo ya ce ya san matsalar da ta kawo cikas ga fara aikin samar da wutar lantarki na Mambila, kuma ya ba da tabbacin cewa zai kawo sauyi cikin kankanin lokaci idan aka tura shi a ma’aikatar wutar lantarki.

Muazu Sambo wanda ke da kimanin shekaru 35 na gogewar aiki a fannin inshora, ya ce yana da kwarewar da ake bukata don taimakawa wajen gyara gibin kayayyakin more rayuwa a kasar.

“Tare da gogewa na a cikin shekaru 35 na hidima da ya shafi fannoni daban-daban, zan taimaka wa shugaban kasa a yunkurinsa na gyara gibin kayayyakin more rayuwa a kasar,” in ji shi.

Mista Sambo ya koka da yadda har yanzu ba’a kammala aikin samar da wutar lantarki na Mambila ba, duk kuwa da irin billiyoyin nairori da aikin ya lakume.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here