Hukumar kula da gudajen gyaran hali ta Najeriya ta ce fursunoni 262 sun tsere daga gidan yarin Jos, babban birnin jihar Filato.
Wata sanarwa da hukumar kula da gyaran halin ta fitar ranar Litinin ta hannun kakakinta Mr Francis Enobore, ta ce fursunoni tara sun mutu yayin da ma’aikacin gidan yarin daya ya rasu, kana aka kashe dan bindiga daya yayin harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a kurkukun ranar Lahadi.
Hukumomi sun ce maharan sun bude wuta sannan suka ci karfin masu gadin gidan yarin kafin su fasa inda fursunonin suke.
An sake kama fursunoni goma da suka tsere, yayin da har yanzu ake neman 252.
Babu tabbaci game da ainihin ‘yan bindigar da suka kai harin da kuma dalilinsu na yin hakan.
Tun da farko, hukumomin sun ce an ritsa da maharan a cikin gidan yarin, amma daga bisani sun ce sun tsere bayan kubutar da daruruwan fursunoni bayan kashe fursuna tara da ma’aikaci daya.













































